1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

190612 Europa G20

Usman ShehuJune 19, 2012

Shugabannin ƙasashen da suka fi karfin masana'antu a duniya wadanda aka sani da G20, sun fara taron duba matsalar tattalin arzikin duniya

An fara taron shugabannin ƙasashen 20 da suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya wadanda aka sani da G20, a birnin Los Cabos dake ƙasar Mexiko. Babban abinda jadawalin taron na su zai mayar da hankali a kai shine matsalar tattalin arzikin ƙasashen da ke amfani da kuɗin Euro. Su dai ƙasashen Turai na ganin cewa Matsalar basukan dake kansu, na nan a sauran ƙasashen duniya, ba wai matsalace ta Turai kawai.......

A jawabin manema labaran da ya gabatar gabanin bue taron, shugabana hukumar Tarayyar Turai Manuel Barroso, ya maida martani kan sukar da ake yi wa ƙasashen Turai cewa, batun farfado da tattalin arzikin su yana tangal-tangal.

"Ba dukkan asashen dake G20 ke da tsarin mulkin demokradiyya, a Turai muna aiki ne da demokradiyya, kuma muna war-ware matsalar sannu a hankali a demokraɗiyyance. A wasu lokutan batun na buƙatar dan lokaci a ƙassashen 27 dake bin tsarin demokradiyya. Don haka a gaskiya bawai mun zo nan bane domin a karantar damu tsarin demokradiya ko na tattalin arziki"

Batun gaskiya dai shine, ƙasashen Turai su suka fi bada kaso mai tsuka a asusun bada lamuni na IMF. Abinda kuma Barroso yace dole a yi adalci ga kowa, ko da kuwa ƙasashen Turai ne suka dace sum a amsar tallafi daga asusun.

"Don haka idan akwai ƙasashen da aka gani suna buƙatar tallafin kudi, ciki harda EU, banga dalliin da zai sa asusun ba zai tallafa ba"

Shi ma dai shugaban Tarayyar Turai Herman Van Rompuy, ya bayyana cewa ƙasashen EU na da ƙwarin gwiwa bisa sakamkon zaɓen ƙasar Girka, amma ya ƙara da cewa

"Wannan rikicin na ƙasashen dake amfani da kudin Euro, zai ɗau lokaci kan a war-ware shi, babu wani abun gaggawa. Amma dai za mu yi duk iya ƙarfinmu, don ganin bayansa"

Ita ma dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ra'ayin ta ya zo ɗaya dana Rompuy, inda tace taron na Mexiko yakamata ya fito da tsarin bai daya, da za abi, wajen war-ware matsalar sannu a hankali.

"Anan yakamata ko wace nahiya ta war-ware matsalar ta. Mu a Turai abinda muka sa a gaba kenan. A Turai za mu ɗau mataki na bai ɗaya, ta yadda za mu haɗa kai mu war ware rikicin ƙasashen masu amfani da euro, a tsakanin mu yamu dake Turai"

Irin waɗannan kalaman ƙarfafa gwiwa dai sune ki fitowa daga taron na G20 bawai daga ƙasashen Turai kawai ba, amma misali shugaban ƙasar Amirka Barack Obama, ya nuna ƙwarin gwiwarsa yayinda yake ganawa da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel. Shi ma shugaban ƙasar Mexiko Felipe Calderon wanda shine mai ma sauki baƙi, ya jinjinawa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, bisa tsayin dakar ta na ganin an war-ware rikicin kudin na Euro.

Mawallafa: Christina Bermann / Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu