1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

110111 Sudan Referendum

January 11, 2011

Sabon sunan da za'a raɗawa ƙasar da samun daidaito a rabon madafan iko a tsakanin ƙabilu 67 dake kudancin ƙasar na daga cikin ƙalubalen da za ta fuskanta bayan ayyana 'yancin cin gashin kai

Shugaban kudancin Sudan Salva Kiir a lokacin kaɗa ƙuri'aHoto: AP

A ranar lahadin da ta wuce ne al'umar kudancin Sudan suka fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen raba gardama wanda za'a shafe tsawon mako guda ana gudanarwa wanda kuma zai shata sabon babi a tarihin ƙasar. Akwai dai ƙalubale masu yawa da yankin zai tunkara Idan mafi rinjayen jama'ar suka zaɓi ɓallewa daga arewacin ƙasar domin kafa yantacciyar ƙasarsu. Abdullahi Tanko Bala na ɗauke da ƙarin bayani.

Ƙalubalen dai sun haɗa da tsara shin menene makomar ƙasar za ta kasance a gaba? Sannan akwai batun shata muhimman alamu na sabuwar ƙasar kamar Tutar ƙasa da ranaikun hutu dama sunan da za'a riƙa kiran sabuwar ƙasar da kuma tsara manufofin dangantaka da ƙasashe maƙwabtanta dama kuma manofofin ƙetare da gamaiyar ƙasa da ƙasa.

Ga yan kudancin ƙasar wannan babban abin alfahari ne. A birnin Juba dake kudancin Sudan matsan yankin na sha'awar wasan motsa jiki na ƙwallon raga inda a yayinda suke wasannin a waje guda kuma suna sauraron waƙoƙi domin nishaɗantarwa.

Ɗaruruwan mutane kan ziyarci filin ƙwallon da maraice domin kallon wasanin. Ga misali a wannan rana ƙungiyar ƙwallon raga ta Black Stars ce ta kara da takwararta ta Warriors a gasar ƙarshe ta cin kofin Bifam.

Jama'ar kudancin Sudan cikin murna da farin cikiHoto: picture-alliance/dpa

Bill Dueni shahararren ɗan wasan ƙwallon raga na NBA na kai komo a tsakanin ƙungiyoyin biyu. Mai shekaru 26 da haihuwa ya girma ne a Amirka kuma a yan watannin da suka gabata ne ya kai ziyara mahaifarsa a kudancin Sudan. Kafin zuwansa Amirka ya kan yi wasan ƙwallon raga tare da takwarorinsa a kudancin Sudan.

" A kudancin Sudan ana sha'awar ƙwallon raga kamar yadda ake sha'awar ƙwallon ƙafa, mutane na sha'awarsa sosai musamman matasa. Sai dai abin takaici shine wasan bai sami cigaban da ya kamata ba saboda tsawon shekaru 20 da aka yi ana yaƙi. To amma fa muna son wasan fiye da yadda ake tsammani. Shahararrun 'yan wasan ƙwallo daga kudancin Sudan kan yi amfani da wasan ƙwallon raga wajen jan hankalin al'uma a lokacin yaƙin domin faɗakar da su game da halin da kudancin ƙasar ke ciki".

A taƙaice dai wasannin motsa jiki ka iya kasancewa wata muhimmiya ta hanya ta haɗa kan al'umar kudancin Sudan domin zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Wannan shine babban ƙalubalen da za'a yi ƙoƙarin cimma a nan gaba.

Akwai dai matsaloli har yanzu musamman na cikin gida a tsakanin ƙungiyoyin ƙabilu 67 waɗanda ke zaune a yankin waɗanda kuma dukkaninsu ke magana da harsuna daban daban da kuma ɗabi'u da al'adu daban daban. Ba dai abu ne mai sauƙi ba samun shauƙi na ƙaunar ƙasa a tsakaninsu duka, kamar yadda Farfesa Madut Jok Jok masanin tarihi wanda ya yi karatunsa a ƙasar Amirka ya nunar. Madut Jok wanda a yanzu sakatare ne a ma'aikatar wasanni da raya al'adu a kudancin Sudan ya bada shawarar abin da yake gani ya kamata a ɗauka a matsayin babbar alamar ƙasar.

Jama'ar kudancin Sudan wajen zaɓen raba gardamaHoto: picture alliance/dpa

" Ƙasa tana ginuwa ne ba wai ƙirƙirarta ake yi ba, a saboda haka idan kudancin Sudan ya sami yancin kansa tilai ne a buƙaci ƙarfin zuciya domin gina ƙasar. Ko da yake wannan abu ne mai wahala bisa la'akari da yawan ƙabilun da ake da su da kuma rigingimu kan albarkatun ƙasa. To amma muna buƙatar haɗin kai kuma jama'a za su yi farin ciki idan suka ga suna da wakilci ta fuskar al'adu da kuma addininsu a cikin al'amuran ƙasa.

A haƙiƙa dai akwai jan aiki a gaba musamman ga sabuwar ƙasar wadda yawancin shugabaninta da harkokin tattalin arziki ke hannu ƙabila guda mafiya rinjaye wato ƙabliar Dinka. Shi kansa shugaban ƙasar Salva Kiir Mayardit ɗan ƙabilar ta Dinka ne haka zalika yawancin Ministocinsa da manyan hafsan soji dukkaninsu 'yan ƙabila ɗaya ne. A saboda haka abu ne mai matuƙar muhimmanci idan ƙasar ta ayyana yancin cin gashin kai a samu daidaito na rabon madafan iko na sabuwar gwamnatin a tsakanin ƙabilun yadda kowace ƙabila za ta ji cewa tana da wakilci kuma ana damawa da ita.

Ana iya sauraron sautin rahotanni akan ƙalubalen zaɓen raba gardamar da kuma hira da wakilinmu a SudanShuaibu Yunus akan yanayin tsaro wajen gudanar da zaɓen raba gardamar.

Mawallafa: Simone Schlindwein/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal