1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarfafa hulɗa tsakanin Jamus da China

January 7, 2011

Ƙasar China ta buƙaci inganta hulɗar ciniki tsakanin ta da Tarayyar Jamus, ƙasar da ke da tasiri a fitar da haja ƙasashen waje.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke tattaunawa da Firimiyan China Wen JiabaoHoto: picture-alliance/ dpa

A jiyane mataimakin firai ministan China Li Kettschi'ang ya fara ziyar kwanaki uku a ƙasar Jamus da zimmar ƙarfafa hulɗar siyasa da kasuwanci, tsakanin ƙasashen biyu mafiya sayar da haja a ƙetare. Daga isowarsa dai ya gana da ministan tattalin arzikin Jamus Rainer Brüderle, wanda ya jaddada kiran Chnina ta ƙara darajar kuɗinta bisa na euro. A yanzu dai wani lokacine da ƙasashen EU da Amirka suke taƙaddama kan zargin da ake yi wa China, na rage darajar kuɗin ta da wata manufa. Da yake ganawa da 'yan kasuwan Jamus, Li yace China ta na buƙatar ƙarfafa hulɗa da ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro, domin suna da mahimmanci ga kasuwannin duniya dama na China. A yaune ake saran mataimakin firimiyan Chinan, zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas