1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarfafa taimakon jin ƙai ga al'umar Siriya

October 1, 2012

Minsitan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yi alƙawarin ƙara taimakon jin ƙai ga Siriya.

Hoto: Reuters

A dangane da mummunan faɗan dake ci gaba da gudana a ƙasar Siriya, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ɗauki alƙawarin ƙarfafa ba da taimakon jin ƙai ga ƙasar ta Siriya. Bayan wata ganawa da takwarar aikinsa na Faransa Laurent Fabius a garin Müllheim dake jihar Baden-Württemberg, Westerwelle ya ce saboda halin da ake ciki a Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya abin da aka sa gaba yanzu shi ne taimaka wa al'umar Siriya. Ya ce muhimmin abu ne talafa wa 'yan adawar Siriya, sai dai bai yi ƙarin bayani ba. A nasa ɓangaren ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius kira yayi ga 'yan adawar Siriya da su haɗa kai, ya ce a kan haka za a tatauna a tarukan da za a yi a Doha da birnin Marakesh na ƙasar Maroko. Ya ce rikicin Siriya ya zama wani mummunan bala'i ne da ƙabilar shugaba Bashar al-Assad suka haddasa. Da aka tambaye shi ko Faransa za ta taimaka wa 'yan adawa da makamai sai Laurent Fabius ya ce a'a.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu