1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙaruwar zaman ɗar-ɗar tsakanin Isra'ila da Hamas

July 4, 2014

Bayan garkuwa da kuma kashe matasan Isra'ila uku da kuma kashe wani matashi Bafalasɗine, an shiga zaman zullumi a Gabas ta Tsakiya.

Jerusalem Begräbnis ermodeter Jugendlicher 04.07.2014
Hoto: Reuters

Matasan Falasɗinawa sun yi arangama da 'yan sandan Isra'ila a lokacin jana'izar matashin ɗan Falasɗinu a unguwar da ya zauna. Dubban mutane ne dai suka taru a wurin jana'izar a lokacin da masu makoki suka ɗauko gawar matashin ɗan shekaru 16 daga wani masallacin gabashin Birnin Kudus zuwa maƙabartar da ke kusa. Wannan dai na zuwa ne a lokacin da zaman fargaba ke ƙaruwa a yankin na Gabas ta Tsakiya.

An dai yi ta hayaniya da kuma harba hayaƙi mai sa hawaye gabanin jana'izar ta Mohammed Abu Khdeir da Falasɗinawa suka ce Isra'ilawa masu matsanancin ra'ayi suka yi wa kisan gilla. Jana'izar ta kuma zo ne a Jumma'ar farko ta azumin watan Ramadan na bana. A ranar Laraba aka ga gawarsa a ƙone cikin wani daji bayan an sace shi kusa da gidansu. Kisan na matashin kuma ya zo ne kwanaki biyu bayan gano gawarwakin wasu matasan Isra'ila uku da su ma aka yi wa kisan gilla, kisan da Isra'ila ke zargin Hamas da hannu a ciki.

Fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas

Hoto: Reuters

Halin da ake ciki na barazanar rikiɗewa zuwa wani yaƙi musamman tsakanin Isra'ila da Hamas wadda ke harba rokoki cikin Isra'ila. A kan haka Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi gargaɗi da cewar.

"Muna da zaɓi biyu. Idan aka daina harba rokoki cikin kudancin Isra'ila, za mu daina kai farmaki. Amma idan aka ci gaba da harba rokoki ka unguwanninmu, to dakarun da ke can za su mayar da martani mai ƙarfi."

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafa: Ulrike Schleicher / Mohammad Nasiru Awal
Edita : Abdourahamane Hassane