Ƙasar Estoniya za ta fara yin amfani da takardar kuɗin Euro
July 13, 2010![](https://static.dw.com/image/4526155_800.webp)
Talla
Ministocin kuɗi na Ƙungiyar Tarayyar Turai sun amince da ƙasar Estoniya ta fara yin amfani da takarda bai ɗaya ta kuɗin Euro a farkon sabuwar shekara mai shirin kamawa.
Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe ga ƙasar ta Estoniya na zamewa memba dindindin a cikin Ƙungiyar Tarayyar Turai.
Ƙasar wacce ke a arewa maso gabacin Tarayyar Turai ta shigo ne a cikin ƙungiyar tun a shekara ta 2004, bayan da ta ɓalle daga Tarayyar Soviet a shekara ta 1991, kuma ita ce ƙasa ta 17 a nahiyar ta Turai da za ta yin amfani da takardar kuɗin Euro .
Mawalafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal