Ƙasar Libiya na fama da ƙaranci abinci
July 5, 2011Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato PAM ta ce gomai na duban jama'a a ƙasar Libiya na fama da ƙaranci cimakka,Hukumar wacce wasu wakilan ta suka kammala wata ziyara a lordinan Nalout da Wazin da Jadu da kuma Zintan dake a yankin yammaci ta ce jama'ar suna cikin wani mawuyacin hali na matsi inda shaguna da kantuna suke a kule,sannan kuma ma'aikatan gwamnati ba a biyashesu ba kuɗaɗen albashi ba tun cikin watan feberu da ya gabata.
Itama ƙungiyar Red Cross ta baiyana fargaban ta akan rashin kayayyakin aiki da magungunan a cikin asibitoci inda kuma ake fama da ƙarancin mai'aikata.A halin da ake ciki kuma wani harin da dakarun kanal Muammar Gaddafin suka kai a garin Misrata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha ɗaya
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar