1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Nijar ta amince da 'yan tawayen Libiya

August 27, 2011

Hukumomin Nijar sun ce tilas ne su samu hulɗa ta gari da ƙasar Libiya wacce ke zaman babbar maƙobciya

Mahamadou Issoufou shugaban ƙasar NijarHoto: picture alliance / dpa

Gwamnatin ƙasar Niger ta ba da sanarwa amince da majalisar riƙon ƙwarya ta wucin gadi ta yan tawayen Libiya. A cikin wata sanarwa da gidan rediyon ƙasar ya baiyana ya ce gwamatin ta yi na'ame da canji da aka samu;Bazum Mohammed ministan kula da harkokin waje na ƙasar ya shaidda cewa tilas ne su samu kyaukyawan dangantaka da Libiya dake zaman babbar maƙobciya.

Ƙasashen kusan guda goma ne na nahiyar Afirka suka riga suka amince da sabuwar gwamnatin ta Libiya;a taron da ta gudanar a ranar juma'a da ta gabata ƙungiyar Tarrayar Afirka ta ƙi ta amince da majalisar riƙon ƙwarya a matsayin sabuwar gwamnati

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar