1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Norway mai tarin albarkatun ƙasa

August 11, 2011

Norway tana amfani da tsarin Majalisar dokoki da kuma na sarauta a haɗe, sa'an nan kuma ta fi kowace ƙasa sarrafa man fetur da iskar gas baya ga ƙasashen da ke Yankin Gabas Ta Tsakiya.

Frime Ministan Norway Jens StoltenbergHoto: dapd

Norway tana arewacin Turai ne wato arewa maso yammacin yankin Scandanavia kuma tana da Iyaka da tekun arewa wato North Sea da ke kudu maso yamma sanan kuma da tekun North Atlantic daga arewa maso gabashi. Tana da dogon Iyaka da ƙasar Sweden daga gabas, da wata gajerar iyakar da  ƙasar Finland daga arewa maso gabas har ila yau kuma da Rasha, ita ma a arewa maso gabashi. Norway tana daga cikin ƙasashenTurai da suka fi yawan duwatsu a yankin na Scandanavia. A zamanin jahilliya gaba ɗayan ƙasar na rufe ne da ƙanƙara, kuma wannan ƙanƙara idan ta narke, malalar da ta kan yi ita ce ta kai ga fitar da wasu hanyoyin ruwa daga tekun waɗanda suka yi suna a duniya waɗanda kuma aka fi sanin su da Fjords a turance. A yanzu haka dai da zarar aka ambaci  Norway da waɗannan hanyoyin ruwan na Fjords sukan zo zuci.

Tutar Norway

Tsarin Mulkinta

Ƙasar Norway tana amfani da tsarin mulkin majalisar dokoki da kuma tsarin sarauta. Sarki Herald na biyar shine ke zaman shugaban ƙasa a yayin da Jens Stoltenberg shine Frime Minista. Gwamnatin na da ƙarfi a tsakiya, sa'an nan ta raba sauran sassan ƙasar zuwa matakai biyu, wato Counties a turance wanda ke zaman ƙaramar hukuma sai kuma Municipalities wanda ke zaman jihohi. Duk da cewa bata amince da shiga ƙungiyar Tarayyar Turai ko bayan da ta kaɗa ƙuri'ar raba gardama har sau biyu ba, Norway tana da kyakyawan dangantaka da ƙasashen Turai da Amurka kuma tana ɗaya daga cikin ƙasashen da ke bada gudunmawar dakarun ta zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ma sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

Hasali ma dai tana daga cikin ƙasashen da suka ƙirƙiro ƙungiyar ƙawance ta NATO da Majalisar zartarwar Turai, da majalisar zartarwar ƙasashen arewacin Turai sa'anan tana cikin mambobin yankin tattalin arziƙin Turai da ƙungiyar cinikayyar duniya da ma ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙi da ci-gaban rayuwarsu ta yau da kullun wato OECD sa'an kuma tana amfani da yarjejeniyar Schengen.


Hoto: Fotolia/cybercrisi

Yanayin hasken rana da banbancin lokaci.

Wasu yankunan Norway da ke kusa da doron duniya sukan sami hasken rana da ƙarfe 12 na dare da kuma duhu a lokacin hunturu amma daɗewan duhun ko kuma hasken rana ya danganci matsayin kewayawar doron ƙasa. Daga 19 ga watan Afrilu zuwa 23 ga watan Ogosta akan sami wannan hasken ranan, sai kuma akan sami duhun huturun tsakanin 27 ga watan Oktoba zuwa 14 ga watan Fabrairu. Ba'a samun duhun hunturun a kan ƙasa mai dausayi, domin akan ɗan sami hasken rana na wasu 'yan sao'i to sai dai akwai wani lokacin da ba'a samun hasken ranar ko ɗaya.

A  kudancin ƙasar ma akan sami banbance-banbancen yanayin musammanma a birnin Tormso wanda ke zaman birni na bakwai mafi girma a ƙasar wanda kuma yayi suna saboda wannan yanayi. Akan dai sami hasken rana har zuwa 12n dare ne a tsakanin 17 ga watan Mayu da 25 ga watan Yuli. Sa'annan a sami duhun tsakanin 26 ga watan Nuwamba da kuma 15 ga watan Janairu.

A Oslo babban birnin ƙasar, rana ya kan tashi ne da ƙarfe 03:54 na asuba sa'annan ta faɗi ƙarfe 22:54 wurin sao'i 19 ke nan da hasken rana, lokacin bazara amma a lokacin hunturu rana takan fito ƙarfe 09:18 ta kuma faɗi da ƙarfe 15:12 wato sao'i 7 ke nan na hasken rana.

Hoto: picture-alliance/ ZB

Yanayin Muhalli

Yanayin Norway yana da ɗan ɗimi ba kamar yadda aka zata ba, ya kuma kasance haka ne sakamakon igiyar ruwan tekun Atlantic wadda ke shiga tekun Norway ya kan ɗimama yanayin. Yanayin yanzu ya fi na da zafi kuma akan alaƙanta hakan da ɗumamar yanayi. Saboda a tsakanin shekarar 1990 zuwa 2010 wasu wuraren da a lokacin hunturu akan samu sanyin degree 1-2.5 na ma'aunin Celcius a watan Yuli kuma a sami degreee ɗaya bisa ma'aunin Celcius a wuni ɗaya wato sao'i 24, a kwanakin nan akan sami aƙalla degree 2.4 ƙasa da sifili a ma'aunin Celcius, wato -2.4° Celcius a turance, a kowace rana a yayin da a watan Yuli ko kuma lokacin bazara akan sami degree 17 da ɗigo hutu a wuni ɗaya.


Mallakar Albarkatun ƙarƙashin Ƙasa.

Norway tana da ajiya na man fetur da iskar gas da ma'adinan ƙasa da, itatuwan yin katako, abincin ruwa da wutar lantarkin da ke amfani da ruwa. Idan aka yi amfani da abun da ƙasashen duniya ke sarrafawa a kowace shekara Norway ce ta fi kowace ƙasa sarrafa man fetur da iskar gas baya ga ƙasashen Yankin Gabas ta Tsakiya. Haka nan kuma sashen albarkatun man fetur ɗinta ta ci kashi ɗaya bisa huɗu na abubuwan da ƙasar ke sarrafawa a kowace shekara. Ƙasar tana da sauƙaƙƙaƙen tsarin kiwon lafiya da na illimi da kuma kyakyawan tanadi na kare alumma. A tsakanin shekarar 2009 zuwa 2010 ƙasar ce ta zo na ɗaya a tsarinta na kula da harkokin raya ɗan adam

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Umar Aliyu