1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200810 UNO Pakistan Hilfe

August 20, 2010

Ban Ki-Moon ya ja hankalin kasashen duniya domin a taimakawa Pakistan

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moonHoto: AP

A babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ya guadana ranar Alhamis a birnin New York domin ƙara jan hankalin duniya game da bukatar taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta tagayyara a Pakistan, ƙasashe da dama sun amsa kiran inda suka sanar da ƙarin gudunmawar agaji.

Tun farko dai Majalisar Ɗinkin Duniyar ta buƙaci taimakon gaggawa na tsabar kuɗi Dala miliyan 460 domin tallafawa mutane da bala'in ambaliyar ruwan ta tagayyara, kuma a cewarta mutane fiye da miliyan huɗu sun rasa muhallansu yayin da wasu mutanen miliyan takwas kuma sun dogara ne ga gudunmawar agajin na gaggawa kamar yadda sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya baiyana.

" Pakistan sannu a hankali ta na fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwan Tsunami wadda tasirin munin ke ƙaruwa da kuma bunƙasa".

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar Ban Ki-Moon ya yi ƙoƙarin fahimtar da ɗaukacin mahalarta taron na musamman akan ambaliyar ruwan Pakistan, inda ya sanar da su cewa lokaci na ƙurewa kuma ana buƙatar kuɗin cikin gaggawa. Dala miliyan 460 ne dai hukumar taimakon agajin gaggawa ta Majalisar Ɗinkin Duniyar ta sanar tun da farko a lokacin da ta nemi ɗaukin  gamaiyar ƙasa da ƙasa. Ko da yake an sami fiye da rabin wannan adadi wanda ƙasashe suka yi alƙawarin bayarwa, sai dai a cewar Ban Ki-Moon akwai buƙatar cika waɗannan alƙawura a zahirance.

" Tuni dai muka sami fiye da rabin adadin kuɗin wato kimanin kashi 60 cikin ɗari na abin da ake buƙata, godiya ga karimcin da manyan masu bada gudunmawa suka yi, sai dai kuma dukkan waɗannan alƙawura ana buƙatarsu kuma yanzu ne lokacin buƙatar.

Ban Ki-Moon yace baya ga mutane miliyan takwas da suke bukatar agajin gaggawa kiyasi ya nuna mutane fiye da miliyan 20 ne wannan ambaliyar ruwa ta shafa.

" Wannan adadi ya haura baki ɗaya yawan mutanen da ambaliyar ruwan tsunami na tekun India ya shafa da girgizar ƙasar Kashmir da bala'in guguwa da ambaliyar ruwan Nargis da kuma girgizar ƙasar Haiti idan aka haɗe su baki ɗaya".

Taimakon abinci ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a PakistanHoto: AP

Kasancewar har yanzu ana cigaba da sheƙa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya kuma zai cigaba har zuwa wasu makonni nan gaba, alumar Pakistan na fargabar ta'adin da zai sake haifarwa. A saboda haka ne Ministan harkokin wajen ƙasar ta Pakistan Mahmood Qureshi yace ƙasar na buƙatar taimakon gamaiyar ƙasa da ƙasa.

" Girman ƙalubalen ya fi gaban a baiyana, a taƙaice dai lamarin ya fi ƙarfin ko wace ƙasa mai tasowa ta ce za ta iya tunkararsa ita kaɗai. Muna fata ƙasashen duniya za su yi hanzarin kawo mana ɗauki".

A lokacin wannan taro dai ƙasashe da dama sun yi alƙawarin bada ƙarin gudunmawa kama daga magunguna zuwa sufuri. Alal misali jirage masu saukar ungulu sun yi ƙaranci, kuma hanya ɗaya tilo da za'a iya kaiwa ga wuraren da ambaliyar ruwan ta mamaye shine ta jiragen sama. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ita ma ta yi alƙawarin Washington za ta bayar da ƙarin gudunmawar wasu miliyoyin daloli.

" Bayan alƙawarin ƙarin Dala miliyan 60 da na sanar a yau, Amirka za kuma ta bada gudunmawar sama da Dala miliyan 150 ga asusun taimakon jin ƙai na ambaliyar ruwan".

Bugu da ƙari Clinto ta kuma yi kira ga yan ƙasarta da su ma su bada ta su gudunmawar duk da cewa halin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar ba abu ne mai sauƙi ba.

" Ina so mutanen Pakistan su sani cewa Amirka za ta kasance da ku a wannan mawuyacin hali, za mu kasance da ku a wannan lokacin da koguna ke tumbatsa, za mu kasance da ku a yayin da kuke ƙoƙarin gyara hanyoyinku tare da tunkarar ƙalubalen sake gina ƙasarku da makoma ta gari".

Ita ma gwamnatin  Jamus ta bada ƙarin gudunmawar euro miliyan goma wanda ya kawo adadin taimakon da ta bayar ya zuwa euro miliyan 25. Ministan tarayya Wener Hoyer wanda ya wakilcin gwamnatin a birnin New York ya kuma yi bayani da cewa.

" Ina da matuƙar muhimmanci yadda a wannan taron muka fara shiri game da babban taron da za'a yi nan gaba a watan Satumba da Oktoba domin samo hanyoyin matsalolin taimakon jin ƙai wanda za ƙunshi matakai na gajeren zango da kuma na dogon zango wannan zai taimaka mana sosai ganin cewa nan da yan makonni za'a fara wannan taro".

A cikin watan Satumba ne dai sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar Ban Ki-Moon zai kira wani babban taron majalisar tare da shugabanin ƙasashe domin tattauna matakai na gajeren zango da kuma na dogon zango domin ayyukan jin kai a yayin da aka sami aukuwar annoba. A watan Oktoba ne kuma za'a gudanar da wani taron a birnin Brussels kan yadda za'a haɗa ƙarfi wuri guda domin gina ƙasar Pakistan.

Mawallafa : Lena Bodewein / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu