Ƙasashen Afirka na fafutukar yaƙi da Boko Haram
May 31, 2014Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun yi alƙawarin haɗa hannu domin yaƙar 'yan ta'adda. Shugabannin sun sanar da haka yau Asabar a birnin Accra na ƙasar Ghana, a kwana na biyu na taron da shugaban Ghana John Dramani Mahama, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar ECOWAS ya kira.
Taron ya tattauna hanyoyi da za a bi a yaƙi ƙungiyoyin 'yan bindiga da ke a arewacin Mali da Ƙungiyar Boko Haram a Najeriya. Shugabannin na ƙasashen na yankin yammancin Afirka da suka taru a birin Accra sun yi alƙawarin kafa wata hukumar haɗin gwiwa da za ta yi aiki a tsakiyar Afirka, domin ganin bayan 'yan ta'adda.Yanzu haka dai baya ga batun Boko Haram, akwai rikicin ƙabilanci da na addini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ga kuma rikicin abzinawa a arewacin Mali.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdourahamane Hassane