1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen duniya sun yi alƙawari tallafawa 'yan tawayen Libiya

September 1, 2011

A birnin Paris ƙasashen duniya da suka hallara a taron da aka yi wa laƙabi da taron masu ɗasawa da 'yan tawayen Libiya, sun yi alƙawarin tallafa wa 'yan tawayen, domin sake gina ƙasar wanda yaƙi ya ɗai-ɗai ta.

Sakatriyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da wakilan 'yan tawayen LibiyaHoto: dapd

Dammacin Alhamis ne dai aka soma gudanar da taron ƙasashen duniya a kan makomar ƙasar ta Libiya a birnin Paris na ƙasar Faransa. Taron wanda ke samun hallarta shugabanni kusan guda sittin daga ƙasashe daban-daban yana duba yadda za a sake gina ƙasar Libiya bayan kifar da gwamnatin Gaddafi.

Manyan shugabanni dake halalartatn taron bayaga shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy madugu uban tafiya sune David Cameron na Birtaniya da Stephen Harper na Kanada Silvio Berlusconni na Italiya Ban Ki-moon na MDD da Nabil al-Arabiya Sakataran ƙungiyar ƙasashen Larabawa da Hillary Clinton, sannan da wasu ministocin harkokin waje na China da Rasha da kuma Indiya. A nahiyar Afirka akwai Cadi da Mali da Gabon da kuma Senegal, waɗanda dukaninsu shugabanninsu suka hallara a taron na Paris.

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ke jawabi a taron makomar LibiyaHoto: picture alliance/dpa

Ƙasar Afrika ta kudu ita ka dai ce ta ƙauracewa taron domin nuna adawa da matakin amfanin da ƙarfin soja da NATO ke yi a Libiya.

'Yan magana dai sun ka ce gyara ya fi ɓarna wahala a wannan taro shugabannin za su yi ƙoƙarin samun sakin kuɗaɗen ƙasar Libiya daga ƙasashe daban-daban, domin ƙaddamar da aikin sake gina kamfanoni da masana'antu da kuma kai taimakon gaggawa na magunguna da kayan agaji ga jama'ar da suka tagayyara a sakamakon yaƙin ke matuƙar buƙata.

A yanzu dai daga kuɗaɗen ƙasar ta Libiya da wasu ƙasashen suka saki za a iya kyasta su kamar dalar Amirka biliyan 50 yayin dakuma wasu suke kann hanyar sakin kuɗin wanda dama mallakar ƙasar ne.

Ko da shike a fagen daga har yanzu yaƙi bai ƙare ba amma shugabannin majalisar wucin gadi na ƙasar, musamman ma Mustapha Abdul Jalil ya bayyan fatansa na ganin ƙasar ta koma bisa ta farki na demokaraɗiyya da gaggawa tare da taimakon ƙasashen duniya.

Sai dai tuni wata jarida a ƙasar Faransa da ake ƙira Liberation ta ce jagorancin da Faransa ta yi a cikin wannan al-amari na Libiya ya kasance bani kishiri na baka manda, domin kuwa a sakamakon goyon bayan da Faransa ta bayar ga 'yan tawayen na Libiya, Faransa za ta samu kashi 35 cikin ɗari na man fetur ɗin da ake hakowa a ƙasar.

Abinda ministan kula da harkokin waje na ƙasar Alain Jupe ya yi tsokaci a kai yana mai cewa

"Ba ni da masaniya dangane da wannan labari abinda na sani shine cewa majalisar wucin gadi ta 'yan tawayen ta riga ta ce

'Yan tawayen Libiya ke murnaHoto: picture alliance/dpa

a cikin ayyukan sake gina Libiya da za a yi ƙasashen da suka goyi bayansu za su kasance gaba, wannan kuma ina ganin dai-dai ne"

Dama dai ana kallon taron na ƙasar Faransa kamar wani taro na yin watanda tsakanin ƙasashen duniya, inda kowa wace ƙasa za ta samu rabon ta gwargwadon hima da ta bayar haka za ta samu kason ta, kuma ƙasashe irin su Rasha wanda suka yi jinkiri wajan amincewa da majalisar 'yan tawayen za su tashi a tutar babu.

Shi ma dai shugaban cibiyar 'yan kasuwa na haɗin gwiwar Libiya da Faransa Michele Kaza cewa ya ke yi

Kanal GaddafiHoto: dapd

"Ban san wannan yarjejeniya ba sannan a waje ɗaya kuma ina ganin wannan abu ne da ba zai yiwu ba, domin kashi 35 ya yi yawa"

Alla kulli halin dai 'yan tawayen na Libiya suna jiran samun tallafi daga shugabannin duniya, sai dai har yanzu da alama akwai sauran aiki a gabansu, domin a wani jawabin da kanar Muammar Gaddafi ya yi ta gidan talabijin na ƙasar Siriya, Gaddafin an ambotoci yana mai cewa zas u yi yaƙi bakin rai bakin fama sai abinda hali ya yi.

Abinda ko ke saka zullumi ga masu fashin baƙi dake gani cewa anya ko ba za a kai ga irin abinda ke faruwa a ƙasashen Iraƙi da Afganistan ba, lokaci na gaba kaɗai zai tabatae mana da haka.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani