1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen Faransa da Spain da Italiya sun gabatad da wani shiri na sasanta rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya.

November 16, 2006

Ƙasashen Faransa da Spain da Italiya, sun gabatad da wani shiri, wanda suka ce zai kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla a yankin Gabas Ta Tsakiya, musamman tsakanin al’umman Falasɗinu da Isra’ila. A taron da shugabannin ƙasashen uku suka yi a garin Gerona na ƙasar Spain ɗin, Firamiyan ƙasar Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero, mai karɓan baƙwancin takwarorinsa, ya kyautata zaton cewa Jamus da Birtaniya za su amince da shirin su kuma ba da ta su gudummowa wajen aiwatad da shi. A cikin nasa jawabin, shugaba Jacques Chirac na Faransa, ya ce halin da ake ciki a yankuna Falasɗinawan dai ya ƙara muni fiye da kima.

Shirin da ƙasashen suka gabatar, ya tanadi tura wata tawaga ne zuwa yankin don gano wa idanunta, yadda al’amura suke takamaimai, sa’annan shirya wani taron zaman lafiya, wanda zai sami halartar duk ɓangarorin da rikicin yankin ya shafa, da kuma musayar fursunoni. A cikin nasa jawabin, Firamiyan Italiya, Romano Prodi, ya ce shirin burin nasu, shi ne kawo karshen matuƙar wahalhalun da al’umman yankin musamman Falasɗinawa ke huskanta.