Ƙasashen Turai zasu taimaka wa Spain
June 9, 2012Ministocin kuɗi na ƙasahen ƙungiyar Tarayyar Turai waɗanda suka tattaunawa ta waya tarlho, tare da shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya Christine Lagarde , sun ce mai yi wa su baiwa ƙasar Spain,agajin biliyan dubu ɗari a matsin kuɗaɗen ceto domin ta ƙara ƙarfafa jarin bankunanta waɗanda suke fama da basusuka.
Wannan agaji da ƙasahen zasu bayar wanda shi ne na huɗu ga wata ƙasa ta ƙungiyar Tarayyar Turai tun lokacin da aka soma samun matsalar tattalin arziki a nahiyar a shekara ta 2009.Bayan ƙasashen Girka da Irlande da kuma Portugal na zaman ceto na tattalin arziki mafi tarifi da ƙasahen suka yi.Nan gaba ne ƙasar ta Spain za ta gabatar da buƙatar samin kuɗaɗen ga ƙungiyar.Kuma wasu majiyoyin daga ƙungiyar sun ce matsayin Asusun ba da Lamuni na Duniya akan ƙasar ta Spain zai kasance na larwai ne kwai.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi