1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen yamma na muhauwara game da matakin da za su ɗauka kan Libiya

March 9, 2011

Dakarun Muammar Gaddafi suna ci gaba da kai hari kan 'yan tawaye a daidai lokacin da farmakin da ake kaiwa don murƙushe masu tayar da ƙayar baya ya yi tsanani.

Rikicin Libiya ya zama wata farfaganda tsakanin marikitanHoto: picture alliance/dpa

Ƙaruwar yawan mutane dake mutuwa da kuma barazanar ɓarkewar wani rikicin 'yan gudun hijira na zama wani ƙalubale ga gwamnatocin ƙetare. Ƙasashen Birtaniya da Faransa na jagorantar wani shiri a Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da wani yankin hana shawagin jiragen saman yaƙi domin hana Gaddafi ci-gaba da kai farmaki ta sama akan al'umarsa. A lokacin da take magana a wannan Larabar jami'ar dake kula da harkokin ƙetare ta Ƙungiyar Tarayyar Turai EU Catherine Ashton ta gargaɗi 'yan majalisar Turai da su yi takatsantsan game da matakan da EU za ta ɗauka.

"Ya kamata mu zayyana abin da muke buƙata domin batun hana shawagin jiragen sama na da ma'anoni daban daban. Tabbatar da an yi amfani da basira akan wannan batun shi ne fatan mu."

Sojojin Gaddafi dai na dannawa kusa da garin Zawiyah dake hannun 'yan tawaye domin sake ƙwace garin dake yammacin ƙasar. Mayaƙan 'yan tawaye sun ce dakarun Gaddafi ne ke iko da hanyoyin shiga garin yayin da jiragen saman yaƙi ke yiwa garin lugudan wuta. A wani labarin kuma wani jirgin saman Libiya da ya ratsa cikin sararin samaniyar ƙasar Girika ya sauka a filin jirgin saman birnin Alƙahira na ƙasar Masar, ɗauke da shugaban hukumar samarwa ƙasar ta Libiya kayakin buƙatun yau da kullum, Manjo Janar Abdel Rahman Ben Ali al Sayyid al-Zawy. Babu dai ƙarin bayani game da wannan tafiyar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu