Shekaru 60 sashen Hausa na DW na yada labarai da rahotanni zuwa kasashen Afirka, wannan ya sa a wannan shiri mun tattauna kan tasirin kafafen yada labarai na kasashen waje a kan kasahen masu tasowa kamar Najeriya. Abdul-raheem Hassan ya tattauna da masa kan shirye-shiryen DW Hausa a Najeriya da irin cigaba da ake samu saboda irin wadannan kafafe.