Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da tilasta miliyoyin mutane yin gudun hijira. Fiye da dalibai 100, sun shiga hannun 'yan ta'adda. Matasa na cikin wadanda matsalar tsaro ta fi shafa a Najeriya, wanda ya zama barazana ga makomar ilimi da sauran abubuwan more rayuwa na yau da kullum.