Ƙoƙarin samun maslaha a rikicin Siriya
June 16, 2013Rasha da ƙasashen yamma za su iya kawar da banbance-banbancen da ke tsakaninsu dangane da rikicin Siriya, kalaman Firaministan Birtaniya ke nan David Cameron bayan da suka yi tattaunawar share fagen taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na G8, tare da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin.
Cameron ya ce taƙaddmar da ke tsakanin Birtaniya da Rasha kan Siriya ba sirri ba ne, amma a yanzu haka, akwai inda ra'ayoyinsu ya zo daidai kuma shi ne halin da talakawan ƙasar ke ciki, haɗe da cewa sun ga irin haɗarin da ke tattare da ɗaukar matakai masu tsauri, kuma idan har suka haɗa kai suka kuma mai da hankali kan wannan batu, babu shakka za su cimma nasara.
Shi ma shugaba Putin ya amince da cewa taron na G8 shi ne kaɗai matakin da ya fi dacewa wajen sassanta rikicin na Siriya, saboda rikici ne wanda mataki na diplomasiyya ne kaɗai zai iya ciyo kan shi.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar