1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin shawo kan rikicin Libiya

June 16, 2011

Mahukunta a Libiya sun bayyana haƙoron cimma sulhu da 'yan tawaye muddin babu sharaɗin saukar Gadhafi daga mulki

Mikhail Marglov Benghazi Libyen
Mikhail Marglov, manzon Rasha na musamman akan lamuran Afirka yayin ziyara a Benghazi ranar 07.07. 2011.Hoto: dapd

Jakada na musamman da ƙasar Rasha ta tura zuwa ƙasar Libiya ya ce firaministan ƙasar ta Libiya ya bayyana masa cewar mahukunta a birnin Tripoli suna gudnar da tattaunawa tare da 'yan tawayen ƙasar dake da hedikwata a birnin Benghazi, tare da bayyana cewar ganawar tana gudana ne a can birnin Paris na ƙasar Faransa. Kamfanin dillancin labaran ƙasar Rasha ya ruwaito cewar gwamnatin shugaba Mouamer Gadhafi ta yi watsi da batun ya sauka daga muƙamin sa a lokacin wata tattaunawar da aka shirya a birnin na Tripoli a wannan Alhamis.

A halin da ake ciki kuma Ƙungiyar tarayyar Afirka ta gargaɗi Majalisar Ɗinkin Duniya cewar hare-haren soji a ƙasar Libiya, wani mummunan lamari ne dake wakana. Tuni dama taron ministocin ƙasashen Afirka ya buƙaci tsagaita buɗe-wuta domin bada damar warware matsalolin ta hanyar siyasa.

Jakadan Birtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya Mark Lyall Grant ya bayyana cewar, mai yiwuwa ba za'a tsagaita buɗe-wuta ba idan har shugaba Gadhafi bai yi murabus ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW