1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin warware rigingimu a ƙasar Libiya

February 22, 2011

MƊD na duba hanyar shawo kan rikicin ƙasar Libiya domin kaucewa ci gaba da zubar da jini

Zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin DuniyaHoto: AP

A yau Talata ce Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ke yin wata ganawar sirri domin tattauna yanayin da ake ciki a ƙasar Libya sakamakon zanga-zangar nuna ƙyamar gwamnatin dake gudana a sassa daban-daban na ƙasar. Wannan kuma ya na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da yin matsin lamba ga shugaban ƙasar Mua'mmar Gaddhafi da yayi murabus. A jiya Litinin ne jami'an diflomasiyyar Libya a Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi ƙira ga sojojin ƙasar su taimaka wajen hamɓarar da shugaban ƙasar Mua'mmar Gaddhafi. Wasu tashoshin telebijin guda biyu sun ruwaito cewar wasu gungun sojojin ƙasar sun buƙaci takwarorin su sojojin su bi sahun jama'ar ƙasar wajen ganin bayan shugaban ƙasar daga mulki.

A can birnin Tripoli, fadar gwamnatin ƙasar kuwa, masu zanga-zanga ne suka yi fito-na-fito da jami'an tsaro a jiya Litinin. Shaidun ganin ido sun tabbatar da cewar jiragen yaƙi sun harbe ɗaruruwan masu zanga-zangar. Hakanan an yi wata taho mu gama a birnin Benghazi, wanda shine na biyu mafi girma a ƙasar. Da safiyar Talatar nan ce kuma shugaban na Libya Mua'mmar Gaddhafi ya bayyana ta tashar telebijin na ƙasar, inda ya yi taƙaitaccen jawabin ƙaryata jita-jitar cewar ya tsere zuwa ƙasar Benezuwela. Shugaban ya yi jawabin ne a wajen fadar sa dake birnin na Tripoli.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar