1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙoƙarin warware rikicin Libiya

May 5, 2011

Wasu ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suna tattauna hanyar kawo ƙarshen yaƙi a ƙasar Libiya

Firaministan Birtaniya Cameron tare da sakatariyar harkokin wajen Amirka Clinton, a lokacin taro akan rikicin Libiya a LondonHoto: AP

Jami'an diflomasiiyya daga ƙasashen da ake damawa da su cikin rikicin Libiya suna ganawa a birnin Roma na ƙasar Italiya, inda suka amince da samar da wani asusu na musamman domin tallafawa 'yan tawayen ƙasar a yaƙin da suke yi da sojojin gwamnatin shugaba Muammar Gaddhafi. Kuɗaɗen da za'a samar ga asusun dai gwamnatin wucin gadi ta 'yan tawayen ƙasar dake da hedikwata a birnin Benghazi ne za ta yi amfani da shi wajen gudanar da harkokinta.

Daga cikin mahalarta taron na birnin Roma, wanda ke bitar shawarar da ƙasashen dake cikin yaƙin suka cimma a baya na samar da kuɗaɗen tallafawa 'yan tawayen dai harda sakatare Janar na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmusen, da kuma jagorar 'yan tawayen Libiya. Tun gabannin fara taron ne kuma sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta bayyana manufar da suka sanya a gaba:

"Ta ce, a yau zamu tattauna hanyoyin da zamu ƙara yin matsin lamba ga shugaba Gaddhafi da kuma muƙarraban ta fuskar siyasa, da diflomasiyya da kuma tattalin arziƙi, ta yanda zamu ɓullo da wani tsarin da al'ummar Libiya za ta yi na'am dashi wajen kawo ƙarshen rikicin ƙasar."

Ɓangarorin da ake damawa dasu cikin rikicin Libiya dai sun haɗa da Amirka da ƙungiyar tarayyar turai kana da ƙasashen dake ƙawance dasu a yankin Gabas Ta Tsakiya da kuma wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa guda biyar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu