Ƙoƙarin warware rikicin Sudan ta Kudu
June 30, 2014A shekara ta 2011 ne dai Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai, sai dai babu alamun zaman lafiya a wannan ƙasa.Rigingimu na cikin gida na jam'iyyar da ke mulki a ƙasar ta Sudan ta Kudu dai ya yi sanadiyyar dubban rayukan mutane, a yayin da wajen miliyan guda suka tsere daga matsugunnensu domin neman mafaka. Batu da ke dasa ayar tambaya dangane da yadda aka kafa tubalin shirin zaman lafiyar wannan ƙasa.
Nazarin masana da ƙwararru a kan rikicin na Sudan ta Kudu
Masana harkokin siyasa da kwararru na danganta wannan matsala da rashin sanya al'ummar ƙasar baƙi cikin tsarin zaman lafiya. A kan haka ne yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu bai yi wani tasiri ba wajen cimma sulhun da ake nema, acewar Jok Madud Jok, wanda ya kafa cibiyar nasarin siyasa a birnin Juba, fadar gwamnatin Sudan ta Kudu:
"Irin wannan yarjejeniyar da kawai ke sasanta manyan masu gaba da juna, yarjejeniya ce da ba ta da goyon bayan sauran mafi yawan al'ummar ƙasar. Kancewar yarjejeniya ce tsakanin su ɓangarori guda biyu da ke yaƙar juna, inda su kadai ne za su raba albarkatun ƙasa bisa ga wannan yarjejeniya da suka rattaɓa hannu, ba tare da masaniya kan yadda za su warware matsalolinsu na cikin gida ba"
Sai dai har yanzu ɓangarori biyu da ke adawa da juna ba sa muradin wakilcin jama'a. Ko wane ɓangaren na ganin cewar yaƙi ne kadai, zai ba shi damar mallake albarkatun Sudan ta Kudu.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourahman Hassane