1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ƙasashen larabawa ta kori Siriya

November 12, 2011

A wani taron gaggawa da ta shirya a Masar Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa ta yanke shawara korar Siriya daga matsayin memba da kuma sa mata takunkumi

Hoto: AP

A taron gaggawar da ƙungiyar haɗin kan Larabawa ke gudanarwa dangane da Siriya a birnin Alƙahira a wannan Asabar, ƙungiyar ta kori Siriya kuma ta nemi sanya mata takunkumi da kuma ƙaddamar da tattaunawar samar da canjin mulki nan ba da daɗewa ba tare da shugabanin adawan ƙasar. Haka nan kuma ta umurci gwamnati a Damascus da ta daina hallaka fararen hulan da basu ji basu gani ba.

Aƙalla mutane 13 suka gamu da ajalinsu a arewa maso yammacin Siriya a wannan Asabar, mafi yawancinsu kuma jami'an tsaro, bisa rahotannin da masu fafutukar kare haƙƙin bil adama suka bayar, na gumurzun da ya biyo bayan canza sheƙan dakarun sojojin ƙasar da dama. A waje guda kuma, harbin bindiga ya tarwatsa lardin Sarakib da Idlib inda jami'an tsaro suka yi wa lardunan ƙawanya, kuma dakarun suka buɗe wuta kan wasu motoci da suka fito daga birnin Homs. Haka nan kuma wasu mutane 14 sun mutu a garin saqba wanda ke kusa da babban birnin Syrian wato Damascus, lokacin wani samamen da dakarun gwamnati suka kai don zaƙulo masu adawa. Ko an ran juma'a jami'an tsaron sun hallaka mutane 23 mafi yawancinsu a birnin Homs inda masu bore suka gudanar da zanga-zanga sun kira ga ƙungiyar haɗin kan Larabawa da ta kori Siriya. Tuni dai ƙungiyar Tarayyar Turai da Amurka suka yaba da wannan mataki da ƙungiyar Larabawar ta ɗauka.

Mawallafiya:Pinado Abdu

Edita: Yahouza Sadisou Madobi