Ƙungiyar EU ta ja kunnen Afganistan
November 12, 2012Ƙungiyar Tarayyar Turai ta katse agajin da take baiwa ƙasar Afganistan na euro miliyan 20, inda ta yi gargaɗin cewa duk agajin tsabar kuɗi da za a baiwa ƙasar to dole sai an ga sauyi mai inganci. Jakadan EU a Afganistan yace tallafin Euro miliyan 20 da aka shirya baiwa ƙasar don inganta fannin shari'a, an dakatar da shine bisa rashin ganin hoɓɓasa daga mahukuntan Kabul. Jakadan yace EU na matuƙar bada mahimmaci wajen tallafawa ƙasar Afganistan, to amma nan gaba duk wani taimakon da za a baiwa ƙasar dole sai da sharruɗa. A watan Julin bana ne aka yi wani taron a birnin Tokyo na ƙasar Japan, inda ƙasashen duniya suka ɗauki alƙawarin tallafin sake gina Aghanistan nan da shekaru biyu masu zuwa. Jakadan EU yace babban dalilin daukar matakin shine, ɓangaren shari'an Afganistan ya gurɓace bisa cinhanci, abinda kuma ke shafar talakawan Afganistan da ma ƙasashe masu bada agaji don sake gina ƙasar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Muhammed Nasir Awal