1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar EU ta yi suka ga matakan da Libiya ke ɗauka kan masu bore

February 23, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi Allah wadar da matakin gwamnatin Libiya na yin amfani da ƙarfin hatsi don murƙushe zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.

Wani sashe na dakarun tsaron Libiya sun shiga jerin masu tayar da ƙayar bayaHoto: AP

Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU sun yi kira da a ƙaƙaba wa shugaba Muamnmar Gaddafi na Libiya takunkumi bisa amfani da ƙarfin tuwo da gwamnatinsa ke ci gaba da yi domin murƙushe zanga-zangar nuna adawa da shi. Shugaban majalisar ƙungiyar, Herman Von Rompuy ya ce wajibi ne a hukunta Gaddafi bisa yin amfani da ƙarfi. Ministocin harkokin wajen ƙasashen Jamus da Italy da Faransa da Spian da Birtaniya sun yi barazanar aza wa Libiya takunkumi .

Duk kuwa da Allah wadai da ake ci gaba da yi daga sassa daban-daban na duniya shugaba Gaddafi ya ƙi sauka daga karagar mulki. A cikin jawabinsa da ke zaman irinsa na farko tun bayan ɓarkewar zanga-zangar shugaban na Libiya ya lashi takobin ci gaba da zama a ƙasar har sai ya yi mutuwar shahada. Mutane ɗari uku ne aka ƙiyasce sun rasa rayukansu i zuwa yanzu. A don haka ƙasashe da dama sun fara kwasan 'ya'yansa daga Libiya. Hukumar zartarwar Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta kwashe 'ya'yanta kimanin dubu goma da a halin yanzu ke ƙasar ta Libiya kafin ranar Alhamis. Gwamnatin Turkiya ta ce tuni ta kwashe 'ya'yanta dubu biyar daga wannan ƙasa, China ita kuma a nata ɓangaren cewa ta yi tana jira ne Libiya ta ba ta izinin kwasan 'ya'yanata dubu 30 da jiragen sama na haya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal