1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Human Right Watch ta zargi 'yan tawayen Libiya da laifin cin zarafin fara fula

July 13, 2011

'Yan tawayen na karkashe jama'a tare da ƙone gidajen su a yankin yammaci na ƙasar da suka karɓi iko da shi

Yan tawayen Libiya masu amfani da manyan makamaiHoto: AP

ƙungiyar Human Right Watch ta shedda cewa 'yan tawaye ƙasar Libiya sun aikata ta'asa da feyade dakuma cin zarafi fararan fula, tare da kwasar ganima a kantuna da shaguna, dakuma ƙona wasu gidajen jamaar a cikin wasu garuruwa fudu dake a yankin yammaci na kasar wanda suka karɓi iko da su a cikin watan jiya.Ƙungiyar ta ce wakilan ta sun tabbatar da wannan laifin a binciken da suka gudanar inda suka riƙa yin tambayoyi ga jama'ar da suka ce yan tawayen sun riƙa lakaɗa masu dukka akan zargin cewa suna goyon bayan kanal Muammar Gaddafi.

Wannan al'amari ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin ƙasar Faransa ta kaɗa ƙuria'a amince wa da tsawaita wa'adin aikin rundunar sojojin ƙasar a Libiya.

Zaɓin wanda 'yan majalisun 482 na jam'iyar dake yin mulki da kuma 'yan adawar suka yi na'ame da shi da gaggarumin rinjayem, baya ga masu ra'ayin kwaminisanci da 'yan fafatukar kare muhali da suka hau kujerar naƙi ,ya zama tilas a cewar fraministan ƙasar Francois Fillons wanda kuma ya ce aikin na da wahala.''ya ce bamu taɓa cewa ba kai harin a Libya wani abu ne mai rangwame, kuma bamu ce ba abu ne da ake iya ƙarewa cikin gajeren lokaci :

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu