1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar NATO za ta inganta matakan kare fararen hula a binin Misratan ƙasar Libiya

April 6, 2011

'Yan tawayen dake yaƙar sojojin Muammar Gaddafi sun zargi dakarun NATO da rashin ba su kariyar da ta dace.

Hoto: dapd

Ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ta yi alƙawarin ba da cikakkiyar kariya ga mazauna birnin Misrata da fama da gamurzu a ƙasar Libiya. Wata mai magana da yawun ƙungiyar ta faɗa a birnin Brussels cewa za a fi ba da fifiko wajen kare rayukan fararen hula. da farko kwamandan 'yan tawayen Libiya Abdel Fattah Yunis ya zargi NATO da cewa ta kai al'umar Misrata ta baro, saboda rashin mayar da martani cikin gaggawa. A kuma halin da ake ciki dakarun Muammar Gaddafi sun fatattakin sojojin sa kai na 'yan tawaye daga garin al-Brega mai tashar jiragen ruwan jigilar man fetir. Kafofin yaɗa labaru sun ce jiragen yaƙin NATO suna shawagi a yankin ba tare da sun yi katsalandan a cikin faɗan ba.

A wani labarin kuma sakataren tsaron Amirka Robert Gates ya fara ziyara a Riyadh babban birnin ƙasar Saudiyya inda zai tattauna da sarki Abdullah akan zanga-zangogin da ake yi a ƙasashen Larabawa da kuma batun sabunta rundunar sojin Saudiyya ta yadda za ta iya kare kanta daga duk wani harin rokoki da Iran ka iya kaiwa. Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta uku da sakataren tsaron Amirkan ya kai Saudiyya a cikin wata guda. Tun bayan ɓarkewar bore a Masar dangantaka tsakanin Amirka da Saudiyya ta yi tsami domin kiran shugaba Barack Obama yayi a lokacin ga tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak da yayi murabus.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar