Ƙungiyar NUJ ta yi jerin gwano a Lagos
August 16, 2012 An gudanar da zanga zangar lumana a lagos bisa cin zarafin yan jarida .
A bisa cin zarafin masu farautar labarai a birnin Lagos yanzu yaci tura inda sai da suka gudanar da zanga zangar lumana don nuna korafi ga abun da ya shafi hukuma. Sun dai kai korafin ne ga fadar gwamnatin jihar ta Lagos da kuma ofishin kwamishinan rundunar yan sandan jihar.
An dai dade ana yiwa yan jaridar romon baka, inda daga bisani sai a mayar da su tura tsohuwar mota. .
Kungiyar yan jarida ce ta Lagos ta dauki nauyin shirya zanga zangar. A makon daya gabata dai wasu yan jarida biyu suka sha kashi a hannun jamma'a a lokacin da suke gudanar da aikin su, inda a yanzu haka suna asibiti inda suke jiyya.
kan haka ne shugaban kungiyar yan jaridun ta NUJ reshen jihar Lagos Mr Deji Elumoye yace ko kadan ba za ta sabu ba. Yace sun fito ne don adawa da irin cin kashin da ake masu a yayin da suke kan aikin su na fadakar da jamma'a abun dake faruwa a kasa baki daya .
Shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa Malam Mohammed Garba yace dole sai an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya. Yana mai cewa har yanzu babu daya da aka kama don ya aikata laifi
Malam Salisu Hamisu Dan jarida ne a Lagos, yace in dai ana san ayi gyara to gwamnati za ta iya yi, amma abun da yake tsakanin gwamnati da yan jarida ta na sane da hakan .
Shi dai Malam Mousa Ibrahim dan jarida cewa yayi a bisa waiwaye adon tafiya, ba yau ba aka fara kashe yan jarida da kuma cin zarafin su ba a Najeriya, illa dai kawai ayi hattara.
Mawallafi: Mansur Bala Bello
Edita: Usman Shehu Usman