Ƙungiyar OSCE ta hango wata barazana a rikicin Ukraine
February 27, 2015Talla
Manzon musamman na ƙungiyar nan ta tsaro da haɗin kan ƙasashen Turai wato OSCE da ke ƙasar Ukraine, ta yi gargaɗi kan yiwuwar ɓarkewar sabon faɗa a Ukraine, a dai dai lokacin da ake batu na tsagaita buɗa wuta a gabashin Ukraine ɗin.
Jami'ar diflomasiyar wato Heidi Tagliyavina, da ta shaidawa kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya cewa akwai alamun dakatar da faɗa a gabashin Ukraine ɗin tare ma da sakin fursunoni da janye manyan makamai, ta ce ta hango alamun taɓarɓarewa lamura a yankin, don a cewarta ko a yau Jumma'a ma sai da aka kashe sojojin Ukraine uku a wata fitina da ta kaure tsakaninsu da 'yan tawaye magoya bayan Rasha.