1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syrien Sanktionen

November 15, 2011

A ci gaba da ɗauka tsauraran matakan kan Siriya, a yau talata ƙungiyar tarayyar Turai ta ƙaƙaba wa wani hafsan sojan ƙasar takunkumin haramcin shigowa nahiyar Turai

Catherine Ashton, mai kula da manufofin ƙetare na Ƙungiyar Tarayyar Turai da Andris Piebalgs, kantoman ƙungiyar aka manufofin raya ƙasaHoto: dapd

Kwamandan soji, da kuma wani Lauya na daga cikin jerin mutane goma sha takwas da ƙungiyar tarayyar Turai, mai ƙasashe mambobi ashirin da bakwai ta sanya wa takunkumin taɓa ƙadarorin su da kuma na tafiye-tafiye, wanda ya kawo adadin mambobin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Siriya da takunkumin ya shafa ya zuwa saba'in da huɗu cikin a watannin baya bayan nan.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta wallafa jerin sunayen mutanen ne yini ɗaya kacal bayan da taron ministocin kula da harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar ya yi zaman faɗaɗa takunkumin da zai hana Siriya samun kuɗaɗe daga bankin zuba jari na tarayyar Turai a matsayin matakin ƙara yin matsin lamba akan shugaba Assad bisa matakan da gwamnatinsa ke ɗauka wajen daƙile masu boren adawa da ita.

Masu zanga-zangar goyan bayan gwamantin Siriya na bayyana adawarsu da shawarar da ƙungiyar haɗin kan Larabawa ta ɗauka da kuma takunkumin ƙasashen TuraiHoto: dapd

Daga cikin jerin sunayen dai har da janar Jumah al-Ahmad, dake zaman babban kwamandan runduna ta musamman dake amfani da ƙarfin daya wuce ƙima wajen far ma masu bore a sassa daban daban na ƙasar ta Siriya. Sai kuma Kanal Luay al-Ali, shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar dake birnin Daraa, wanda aka zarga da ƙaddamar da farmaki akan masu bore a lokacin da zanga-zanga ta kunno kai a ƙasar. Akwai kuma wani na hannunn daman shugaba Assad Janar Aous Aslan dake jagorantar rundunar juyin juya halin ƙasar, kana da kanal Maher, wanda ƙani ne ga shugaba Assad. Hakanan ƙungiyar tarayyar Turai ta sanya sunan wani ƙwararren Lauya mai suna Bassam Sabbagh, wanda ke da wakilci a ƙungiyar lauyoyi ta birnin Paris na ƙasar Faransa bisa abin da ƙungiyar ta ce yana da hannu wajen samar da kuɗaɗen tallafi ga gwamnatin Siriya.

Fitar da jerin sunayen ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar Rasha ta gudanar da wata tattaunawa a birnin Moscow tare da shugabannin 'yan adawar ƙasar, inda ta buƙaci su rungumi hanyar zama kan teburin shawara domin samun biyan buƙatun su, maimakon tashin hankali, abinda kuma ministan kula da harkokin wajen Siriya Walid al-Mouallem ya ce dattakun da China da Rashar ke nunawa ƙasar sa, abin godiya ne:

"Na yi amannar cewar matsayin ƙasashen Rasha da China, waɗanda a kowane lokaci ke tsayin daka wajen kare muradun 'yan ƙasar mu, ba zai sauya ba, tunda muna ci gaba da rungumar hanyar tattaunawa domin shawo kan matsalolin mu."

Can a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya kuwa firaminista Tayyip Erdogan ne ya yi barazanar sanya sunan shugaba Assad cikin jerin shugabannin da ba su ɗauki zubar da jinin jama'a a matsayin wani abu ba, kana ya buƙaci shugaba Assad ya ɗauki matakan cafke waɗanda ke da alhakin ƙaddamar da hare hare akan ofisoshin jakadancin ƙasashen ƙetare ciki kuwa harda na Turkiyya, tunda kuwa kamar yadda ya ce yana ɗaure da mutane da dama a cikin gidajen yari. Sai dai a yayin da ake tababar da yiwuwar ɗaukar matakin soji akan Siriya, shugaban ƙungiyar Larabawa Nabil al-Arabi ya ce akwai wata buƙatar da Siriya ta gabatarwa ƙungiyar inda ya ce:

"Ministan kula da harkokin wajen Siriya ya gabatar mini da wata buƙatar da a ciki shugaba Assad ya nemi ɗaukacin shugabanni da sarakunan ƙasashen Larabawa da su gana tare da tabbatar da cewar duk abinda zai je ya komo za'a warware matsalar da ake ciki ne a tsakanin su kansu Larabawan."

Sai dai a yanzun da ake dakon abinda taron ƙungiyar Larabawan zai zartar a zaman da za ta yi wannan Larabar, a ƙasar Siriyar kuwa, wata ƙungiyar kare haƙƙin jama'a ce ta bayyana cewar kimanin gawarwaki goma sha tara ne aka kawo wani asibiti dake birnin Homs mai yawan tashe-tashen hankula. Ƙungiyar ta bayyana fargabar cewar mai yiwuwa ma ɗaukacin mutanen da aka kashen, fararen hula ne, waɗanda mayaƙan dake goyon bayan gwamnati suka yi garkuwa da su a kwanaki biyun da suka gabata.

Mawallafi/Björn Blaschke/Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal