1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Tarrayar Afirka za ta shirya taro kan ƙasar Somaliya

July 31, 2011

Ƙoƙarin shugabannin ƙasashen nahiyar Afirka domin ceto ƙasar Somaliya daga fari ta hanyar samar da tallafi

Wasu 'yan ƙasar Somalia dake fama da fariHoto: AP

Ƙungiyar Tarraya Afirka ta ba da sanarwa cewa za ta gudanar da wani taro na musammun domin samar da tallafi ga ƙasar Somaliya da ke fama da matsannancin fari. Sanarwa wacce mataimakin shugaban ƙungiyar Era Mwenda ya baiyana, ya ce za su gudanar da taron a ranar tara ga watan Augusta a birnin Addis Ababa na ƙasa Habasha.

Ana sa ran taron zai samu hallarta shugabannin ƙasashen Afirka da kuma sauran ƙasashen duniya masu hannu da shuni. Yanzu haka dai al'amura na ƙara rincaɓewa a ƙasar ta Somaliya saboda yaƙin da ake fama da shi wanda ke kawo cikas wajen isar da kayan agaji. Hukumar UNICEF ta ce sama da yara ƙanana miliyan ɗaya ne ke buƙatar agajin gaggawa a yankin kudancin Somaliya .

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala