1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO Libyen

March 31, 2011

Tun daga ranar alhamis akalar ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya na matakan soja akan Libiya ya koma hannun ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO akan haka shugaban kwamitin soja na ƙungiyar yayi taro da manema labarai a Brussels

Ƙungiyar NATO ta karɓi jagorancin matakan hana shawagin jiragen sama a LibiyaHoto: AP

Kwanaki goma ke nan gungun ƙasashen taron dangi ƙarƙashin jagorancin Amurka suka ɗauki matakin kai hare haren soji ta jiragen sama daban daban, domin kwance wa shugaba Muammar Ghddafi na ƙasar Libya ɗamarar yaƙi, tare da yunƙurin agaza wa 'yan tawayen ƙasar su kifar da gwamnatin da yayi shekara kusan 42 yana jagoranta. Matakin dai ya biyo bayan daftarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartas na ƙaƙaba takunkumin hana shawagin jiragen sama a ƙasar ta Libya da sunan karya lagon shugaba Ghaddafi, wanda ƙasashen duniya suka mayar saniyar ware, tun bayan tirjiyar da yayi na ƙin amincewa da bukatar 'yan tawayen ƙasar da suka lashi takobin ala tilas sai ya bi sahun sauran shugabanni irin su Mubarak na ƙasar Masar da kuma Zainel Abidin Ben Ali na ƙasar Tuinsia da ala tilas suka jefar da ƙwallon mangoro suka huta da ƙuda wajen sauka daga shugabancin ƙasashen nasu. Ƙasashe da dama dai sun soki lamirin ɗaukar matakin sojin akan ƙasar ta Libya, wanda Amurka ke jagoranta tare da ƙasashen Britaniya da Faransa.

Sansanin jiragen saman NATO a ItaliyaHoto: dapd

Da yake jawabi akan karɓe jagorancin ci gaba da aiwatar hare haren da ƙungiyar ƙwanace ta NATO tayi shugaban kwamitin sojin ƙungiyar Admiral Giampaolo Di Paola, ya ce tuni ƙungiyar ta haramta safarar makamai zuwa ƙasar ta Libya tare kuma da ƙoƙarin tabbatar da matakin nan na haramta shawagin jiragen sama, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartas.

NATO ba ta da alaƙa da majalisar 'yan tawaye

An tambayi Di Paola shin ko NATO tana da wata alaƙar haɗin gwiwa da majalisar 'yan tawayen ƙasar wajen ci gaba da kai harin?

"A a, kowa ya sani cewar alaƙar kawai ita ce da wata ƙungiya ta tuntuɓa wacce Majalisar Ɗinkin Duniya ke mu'amulla da ita wato wacce aka yi taro da ita a taron da aka yi London. Wannan ita ce kaɗai alaƙar. Ba ma gabatar da harin mu da haɗin gwiwa da kowa."

Har ila yau an tambaye shi akan batun abin da NATO zata yi idan kotun duniya ta nemi a miƙa mata Ghaddafi, inda nan ma admiral DI Paola yace:

"Wannan ba ya cikin daftarin shekarar 1973, dan haka ba alhakin NATO ba ne wannan, mu aikin mu shi ne tabbatar da daftarin Majalisar Ɗinkin Duniya ko gobe aka samu sauyin magana daga majalisar to ka ga sabuwar magana ke nan dan haka ba ni da iko akan wannan."

Dangane da matakin tabbbatar da hana safarar makamai zuwa Libya kuwa, nan ma dai shugaban kwamitin sojin na NATO cewa yayi:

"Ko yanzu aka ce ga wani jirgin ruwa makare da makamai to babu ko shakka zamu tsayar da shi, kuma zamu hana faruwar hakan, amma dai ina da yaƙinin cewa dukkan ƙasashen ba zasu keta wannan doka ba."

Babu sojan ƙasa na NATO a Libiya

A ƙarshe admiral Di Paola ya ƙarƙare da batun ko akwai sojojin NATO a ƙasa dake bayar da bayanai ga jiragen sama, inda ya ka da baki ya ce babu wasu sojin NATO a ƙasa idan akwai wani soja to ba na NATO yake ba."

Yanzu haka dai kallo ya koma ga rundunar ta NATO domin ganin yadda zata aiwatar da wannan aiki na tsayawa ga yadda Majalisar Ɗikin Duniya ta iyakance ba tare da wuce makaɗi da rawa ba.

Mawallafi: Nasiru Zango

Edita: Ahmad Tijani Lawal