1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙuri'ar raba gardama a Sudan

January 15, 2011

Bayan mako ɗaya na jefa ƙuri'ar raba gardama, al'ummar kudancin Sudan za ta fara jiran sakamakon da ka iya bata 'yancin girka gwamnatin kanta

Wani ɗan kudancin Sudan, riƙe da tutar yankinHoto: picture alliance/dpa

A yau ne ake sa ran kudancin Sudan zata kammala kada kuri'a, a zaben raba gardama, wanda ake kyautata tsammanin zai kai ga samun yancin yankin a matsayin ƙasa mai cin gashin kansa. Yan kudancin kasar kimanin miliyan hudu ne waɗanda aka yiwa rajistar suka fito ƙwan su da ƙwarƙwatan su tun daga ranar tara ga wannan watan domin kaɗa kuri'unsu. Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir wanda daga farko ya yi kashedin cewa kuri'ar raba gardamar ka iya haifar da rashin kwanciyar hankali ya yi bayanin cewa kawo yanzu dai an gudanar da zaɓen a cikin kwanciyar hankali, ko da ya ke, an sami rahotannin tursasawa wasu daga cikin magoya bayan haɗin kan ƙasar a yankunan da ke Bahr El Ghazal. Jamiyya mai ci ta National Congress Party ta yi alƙawarin ɗaukaka sakamakon zaɓen duk yanda ya kasance, amma shugabanin Arewacin da Kudancin ƙasar har yanzu ba su ɗauki shawarar bai ɗaya ba dangane da wasu batutuwar da ke tattare da sarƙaƙiyya, kamar yadda zasu raba kuɗaɗen man fetur, da ma makomar yankin Abiye wanda ke da arziƙin man fetur kuma ya ke kan iyakan da yankunan biyu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Usman Shehu Usman