1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a ƙasar Masar

March 19, 2011

A karon farko, al'ummar Masar na ɗanɗana sahihin zaɓe, a yayin da suke jefa ƙuri'ar raba gardama domin amincewa da gudanar da zaɓuƙan ƙasar a wannan shekarar ko akasin hakan.

An samu cincirindo jama'a a mazaɓuHoto: picture-alliance/dpa

Al'ummar Masar ta cigaba da jefa ƙuri'ar dangane da jerin sauye-sauyen da aka gabatar domin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar. Za'a iya cewa dai wannan shine karon farko da al'ummar ke ɗanɗana sahihin zaɓen, a cikin shekaru da dama. Wannan ƙuri'ar jin ra'ayin, shine matakin farko wajen mayar da ƙasar bisa turbar demokraɗiyya, tun bayan da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati ta hamɓarar da mulkin kama karya na shugaba Hosni Mubarak, a ranar 11 ga watan Febrairu. Waɗanda suka cancanci yin zaɓe, na kaɗa ƙuri'a ne, domin nuna amincewa ko akasin haka game da sauye-sauye guda tara da hukumar da ke da alhakin gudanar da sauye-sauyen ta gabatar. Idan har suka amince, ƙasar za ta gudanar da zaɓn majalisar dokoki da na shugaban ƙasa a cikin wannan shekarar. Idan kuwa ba su amince ba, zai zama wajibi shugabannin sojan su ƙara wa'adin wata shiddan da su ka sanya na miƙa mulki ga farar hula har sai wani tsawon lokacin. Jamiyyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood da wasu 'yan Jamiyyar National Democratic Party na daga cikin waɗanda ke goyon bayan yin zaɓe a wannan shekarar, a yayin da tsohon shugaban hukumar kula da makamashi ta duniya kuma wanda ke neman tsayawa takarar shugaban ƙasa Mohammed El Baradi ke goyon bayan ƙara wa'adin mulkin sojan.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Muhammad Nasiru Awal