Ɓarin wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah a kudancin Labanon
July 25, 2006An cika sati 2 ciccip da ɓarkewar yaƙi tsakanin dakarun Isra´ila da na Hezbollah.
Da sanhin sahiyar yau, an ci gaba da ɓarin wuta mai tsannani tsakani ɓangarorin 2,a yankin Bint Jbeil, a kudancin Labanon.
Sojojin Isra´ila sun bayyana hallaka yan Hezbollah masu yawa, tare da yin assara sojoji guda 2.
A fagen diplomatia,manyan ƙasashe da ƙungiyoyi na dunia na ci gaba da sappa da marwa, da zumar samun tsaigaita wuta.
Bayan ministocin harakokin wajen France, Jamus da Britania , sakatariyar harakokin wajenAmurika Condoleesa Rice, ta ziyarcir Labanon jiya, inda ta gana da hukumomin ƙasar a game da yaƙin.
Saidai an samu rashin fahintar juna, tsakanin Rice, da shugaban Majalisar dokoki Nabih Berry, bayan ta ambata cewar, ba a za a taɓa samun tsaigaita wuta ba,muddun yan Hezbollah, ba su yi belin sojojin Isra´ila 2, da su ka kama ba.
Nan gaba a yau, Condoleesa Rice, za ta ganawa da Praministan Isra´ila Ehud OLmert, kamin ta wuce zuwa Palestinu.
A ɓanagaren Majalisar Ɗinkin Dunia, a na cikintunani akan hanyoyin aika rundunar shiga tsakani a kudanci Labanon.
Gobe ne idan Allah ya kai mu, a birnin Rome na ƙasar Italia za a buɗa taron ƙasa da ƙasa, wanda kacokam zai maida akala, a kan riginginmun da ya ke wakana a yankin gabas ta tsakiya