Ɓarnar girgizar ƙasa a Japan
April 12, 2011Hukumar kula da ingancin nukiliyar ƙasar Japan ta ɗaga matsayin munin ɓarnar da ta faru a cibiyoyin nukiliyar ta ya zuwa mataki na ƙarshe da ya zo dai dai da ɓarnar tashar nukiliya ta Chernobyl ta ƙasar Ukrain a shekara ta 1986. A lokacin daya ke yin jawabi ta tashar telebijin a wannan Talatar, wani jami'in hukumar kula da harkokin nukiliya a ƙasar ya ce hukumar ta ɗaga matsayin ɓarnar daga biyar ya zuwa bakwai. Jami'in, wanda bai bayyana sunan sa ba ya ce yawan tururin dake tasowa a cibiyar nukiliyar Fukushima ya kai kashi 10 cikin 100 na wanda ya tashi a lokacin hatsarin nukiliyar Chernobyl.
A halin da ake ciki kuma - har ya zuwa wannan lokacin, Injiniyoyi basu kai ga nasarar mayar da na'urorin sanyaya tukwanen makamashin nukiliyar Fukushimar ba, wanda kuma zai taka rawa wajen shawo kan matsalar zafin daya wuce ƙimar da tukwanen ke yi. Hakan kuma na nuni da cewar - da sauran jan aiki a fafutukar shawo kan matsalar. Sai dai kuma gabannin sanarwar da hukumar nukiliyar ta yi, an sami wata girgizar ƙasar da bata kai ta Litinin tsanani ba a yankin gabashin Japan - kusa da birnin Tokyo, wadda ƙarfin ta yakai marki shida da ɗigo uku a ma'aunin girgizar ƙasa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman