1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗan sandan Afghanistan ya harbe dakarun NATO huɗu

September 16, 2012

NATO na ci gaba da fuskantar barazana daga Jami'an tsaron Afghanistan da ke yin aiki tare da ƙungiyar.

Afghan policemen keep watch near the remains of a suicide attack victim in the city's diplomatic quarters, home to many Western embassies, in Kabul on September 8, 2012. A teenage suicide bomber struck outside NATO headquarters in Kabul on September 8, killing six people, including child hawkers, as Afghanistan marked a public holiday, officials said. The attack took place as government dignitaries assembled in Kabul to commemorate 11 years since the death of Ahmad Shah Massoud, an iconic anti-Taliban commander two days before 9/11. AFP PHOTO/ SHAH Marai (Photo credit should read SHAH MARAI/AFP/GettyImages)
Hoto: Shah Marai/AFP/GettyImages

Ana zargin wani jami'in ɗan sandan Afghanistan da kissar wasu dakaru huɗu na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO da ke aiki a ƙasar ta Afghanistan, abin da ƙawancen da Amirkar ke jagoranta ke cewar shi ne karo na biyu cikin kwanaki biyu a jere da wani jami'in tsaron Afghanistan ke kissar takwarorin aikinsa na yammacin duniya.

Adadin sojojin ƙetaren da jami'an tsaron gwamnatin Afghanistan suka kashe daga farkon wannan shekarar dai ya kai 51, abin da kuma ke yin barazana ga shirin da ƙungiyar ƙawancen tsaron ke yi na bai wa jami'an tsaron Afghanistan horo, domin ɗaukar alhakin lamuran tsaron ƙasar yayin da dakarun na NATO suka kammala ficewa a shekara ta 2014.

Ko da shike rundunar ƙasa da ƙasa ta ISAF da ke yaƙi a Afghanistan ba ta yi cikakken bayani game da lamarin ba, amma ta ce ya afku ne a yankin kudancin ƙasar ta Afghanistan a wannan Lahadin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas