Ɗaruruwan jama'a a Somaliya na ficewa daga birnin Mogadishu
October 12, 2011Rahotanni daga Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya na cewa ɗaruruwan jama'a na ficewa daga birnin. Domin jin tsoro kada faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen ƙungiyar al-Shabbab.
Da yake magana da manema labarai wani babban kwamandan dakarun gwamnatin kanal Abdullahi Ali Anod ya shaida cewa sun dakatar da ci gaba da kai hare hare cikin 'yan kwanakin nan domin baiwa jama'ar da suka maƙale a cikin wasu unguwanni damar arcewa.
Dakarun gwamnatin riƙon ƙwaryar na Somaliya waɗanda suke samun talafin sojin ƙasashen tarrayar Afirka sun ƙaddamar da wani gagarumin farmaki tun a ranar Asabar da ta gabata a sansanoni na ƙarshe inda 'yan tawayen suka ja daga.
Shedu daga ƙasar sun ce turuwar jama'a ne bisa jakunan wasu cikin motoci da kayayyaki ɗaure cikin ledoji ke ficewa daga birnin na Mogadishu.
Mawallafi: Abourrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal