Barazanar tsaro a Nijar bayan zabe
January 7, 2021Talla
Harin dai na zuwa ne jim kadan bayan kammala zaben shugaban kasa zagaye na farko a Jamhuriyar ta Nijar, da ya bai wa 'yan takara biyu damar sake fafatawa a zagaye na biyu.
Rahonanni sun nunar da cewa kimanin mutane 100 da suka halaka a cikin wani ta’addanci da aka kai a karshen makon da ya gabata a wasu kauyukan kasar da ke kan iyaka da Mali.
Za dai a iya cewa, shekara ta 2021 ta zowa Jamhuriyar ta Nijar cikin yanayin kalubale na harin 'yan ta'adda, baya ga annobar cutar sankarau da ake fama da ita a Damagaram a daidai lokacin da ake fama da annobar cutar coronavirus.