2023: Shekara mai sarkakiya ga dakarun MDD a Afirka
December 27, 2023A kasar Mali, a tsakiyar wannan watan ne dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA suka gudanar da biki a hedikwatarsu da ke Bamako na kawo karshen aikinsu a kasar a hukumance, aikin da ya kunshi sojojin kasashe daban daban har 53. A kasashe kamar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Sudan ta Kudu da Mali da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ma dai, sojojin Majalisar Dinkin Duniya ba su samu wata nasara ta a zo a gani ba. Wasu manazarta sun ce lamaru sun sha wa sojojin kiyaye zaman lafiyaar na Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a karkashin tsauraran dokoki kai a wadannan kasashe.
Karin bayani:Kwango ta raba gari da MONUSCO
Adib Saani, daraktan cibiyar Jatilay ya bayyana takaici da rashin tabuka abin arziki a ayyukan dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a sassan Afirka. Ya ce: "Ta bangarori da dama sun kasa shawo kan tashe-tashen hankula a wadannan kasashe wanda shi ne babban dalilin kai su wurin tun da farko. Babban misali shi ne Mali, wanda har yanzu ba a warware ba, saboda a kullum tashin hankali dada muni yake yi, kuma kamar dai rundunar ba ta za ta iya yin komai ba."
Mali ta raba gari da MINUSMA bisa dalilai na tsaro
A tsakiyar watan Yuni ne gwamnatin mulkin sojin Mali bayan karfafa hulda da sojojin Rasha ta bukaci janye dukkan sojojin kiyaye zaman lafiya 12,000 na Majalisar Dinkin Duniya daga kasar. Hukumomin na Mali sun zargi dakarun kiyaye zaman lafiyar da zama wani yanki na matsalar maimakon tunkarar matsalolin tsaro da suka yi wa kasar katutu.
Karin bayani: Wani hari ya jikkata dakarun MDD a Mali
A cewar Adib Saani babban daraktan cibiyar Jatikay, gwamnatoci kamar Mali su ma suna da laifi wajen gurgunta ayyukan dakarun kiyaye zaman lafiyar. Ya ce: " Majalisar Dinkin Duniya za ta yi nasarar ne kawai idan aka samu kwakkwarar kudiri a yanayin da suke aiki. Amma idan ya kasance babu wannan kudiri, lamarin kan kasance da matukar wahala a gare su. Kuma kasashe kamar Mali alal misali tana tangal-tangal a yanzu da sojoji ke rike da madafun iko. A saboda haka abu ne mai cike da kalubale mai yawa ga Majalisar Dinkin Duniya ta iya gudanar da aiki a karkashin irin wannan yanayi. Sannan abu na biyu akwai rashin yarda a cikin lamarin."
Kalubalen dakarun zaman lafiya na MDD a kasashen Afirka
Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suna da ka'idoji da suka takaita ayyukansu. Misali sojojin kiyaye zaman lafiya ba su da hurumin tilasta aiwatar da wani mataki. Kuma ba a yarda su yi amfani da karfi fiye da kima ko makami mai hadari ba, sai idan ya zama dole don kare kansu ko kuma hurumin da aka bukaci su kare.
Karin bayani: Adawa da sojojin MDD a Kwango
Wasu masana kamar Fidel Amakye Owusu ya dora alhaki kan raunin hurumin da aka bai wa dakarun kiyaye zaman lafiyar, inda ya ce: "Ba zan iya cewa dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka duka sun gaza ba, to amma yanayin hurumin aikin da aka ba su shi ya takaita ikonsu ko kuma tasirinsu a wuraren da ya kamata su yi aiki. A zahirin gaskiya ma dai, dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suna da sharudda da ka'aidoji kuma ba za su iya ketara iyakokin da aka shata musu ba. Kuma a yanayi na tashe-tashen hankula, saboda yanayin tashin hankali a Afirka ba shi da tabbas, kuma ba za iya hasashensa ba, ya sanya aikin kiyaye zaman lafiya a Afirka da matukar wahala. A saboda haka ake gani kamar ba sa yin kokarin da ya kamata a ce suna yi."
Kura-kuran da dakarun MDD suka tafka a Afirka
Sai dai duk da haka, jami'an kiyaye zaman lafiyar su ma ba su yi abin da ya kamata wajen samun aminci da yarda na mutanen kasashen da suke aiki ba. Wasun su an zarge su da aikata fyade da cin zarafi. Majalisar Dinkin Duniyar ta kori sojojin kiyaye zaman lafiya 60 'yan kasar Tanzaniya zuwa gida kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a bana.
Karin bayani: Karfafa dakarun kiyaye zaman lafiya
Wata damuwar kuma ita ce rashin kwanciyar hankali ta fuskar siyasa a wasu kasashe inda dakarun kiyaye zaman lafiyar suke aiki. Kwararru sun ce ana bukatar yin garanbawul a aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya idan har ana bukatar samun nasara a shekarun da ke tafe a Afirka