1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

2023: 'Yan Media sun ce za su daina tallan APC

Nasir Salisu Zango
November 22, 2022

Matasan da ke yada manufofinsu na siyasa a kafafen sada zumunta sun ce za su dakatar da yin hakan har sai jam'iyyunsu sun sauya salo wajen damawa da su sosai in an samu mulki.

Symbolbild I Indien I Soziale Netzwerke
Hoto: Sajjad Hussain/AFP/Getty Images

Tun a baya dai matasan 'yan media sun dade suna ta korafi kan irin yadda suka ce suna tura mota amma daga karshe ta bule su da hayaki, amma wannan korafi nasu ya kara bayyana sosai bayan da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Filato da ke tsakiyar kasar.

Matasan suka ce tsarin da aka bi wajen kai takwarorinsu 'yan fim Filato din a jirgin sama, su kum aka kaisu a motocin haya abin takaici ne. Wannan batu dai ya sanyasu yin tutsu har ma shugaban kungiyarsu na arewacin Nigeria Rabiu Biyora ya saki sanarwar cewar sun tsaya cak yada manufofin jamiyyar APC.

A daura da wannan batu, guda daga cikin 'yan media din wanda yanzu yake kan kujerar shugabancin karamar hukumar Nasarawa a Kano, Auwal Lawal Aronposu, ya ce masu wannan kuka wadanda su ka yi yakin neman zaben shugaban kasa ne a baya ba a yi rabon mukamai da su ba kuma ya ce suna da dalilin kokawa. 

Matasan da ke tallan APC sun ce za su daina don ba a damawa da suHoto: Jaap Arriens/NurPhoto/picture alliance

Da yake maida martani kan wannan batu, hadimin shugaban kasa Buhari a kan kafafen sada zumunta kuma mataimakin daraktan yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu na kafafen yada zumunta, Bashir Ahmad, ya ce ba a mai da masu korafin 'yan bora ba don wasu daga cikinsu sun amfana sosai.

A share guda kuma Mustapha Badamasi Naburaska wanda dan fim ne kuma ake dama da shi a gwamnatin Kano ya ce kansu a hade yake kana ana kula da kowa. Duk da cewar 'yan kungiyar sun tsya cak sun daina yada manufofin jam'iyya amma wata majiya ta tabbatar da cewar an gano bakin zaren nan gaba kadan ma za su janye wannan barazana.