A ƙasar Kenya an sace masu aikin agaji
October 13, 2011A ƙasar Kenya jami'an tsaro suka ce an sace likitoci hudu dake aikin agaji a sansanin 'yan gudun hijara na Somaliya dake iyakar Kenya da Somaliya. Sifeto janar na yan sandan Kenya Leo Nyongesa yace jami'ai sun shiga farauta maharan ta sama da ta ƙasa, kuma kawo yanzu an rufe sansanin yan gudun hijaran wanda shine sanin yan gudun hijira mafi girma a duniya. Shugaban yan gudun hijira a sanin Dadaab, yace biyu daga cikin mutanen da aka sacen turawane dake aikin da ƙungiyar agaji ta Doctors Withiout Boaders, biyu kuma yan ƙasar Kenya ne. Kakakiyar Doktors Without Boaders tace kawo yanzu ba za ta iya tabbatar da labarin ba. Sace mutanen a yau ya biyo bayan sace turawa biyu a jiya, daya dan ƙasar Birtaniya da ba Faranshe, a wurin shakatawa a ƙasar Kenya dake kan iyakarsu da Somaliya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu
AP