A ƙasar Libiya ɓarin wuta ya mamaye Sirte
October 3, 2011A ƙasar Libiya mazauna birnin Sirt na ci gaba da picewa sakamakon fadan da ake yi, tsakanin dakarun gwamnatin wucin gadi da magoya bayan Kanal Gaddafi. Ƙungiyar agajin gaggawa ta Red Cross ta yi gargaɗin cewa birnin Sirte na cikin tsananin buƙatar magunguna, inda ƙungiyar ta kwatanta lamarin da kasance wani mummunan yanayi. Wani jami'in ƙungiyar yace dakarun gwamnatin wucin gadi na cilla rokoki a kan asibitin birnin, a yunƙurin da suke yi na karɓe iko da Sirte. Shugaban gwamnatin wucin gadin ƙasar a jiya yace mazauna birnin Sirte suna da kwanaki biyu don picewa. Waɗanda ke tserewa daga birnin suka ce basu da labarin yarjejeniyar da aka yi, kuma ba a daina ɓarin wuta a birnin ba. Shugaban wucin gadin dai ya sha baiwa mazauna Sirte wa'adi da su pice da yin barazanar ƙaddamar da farmaki, tun a watan Augosta.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas