1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ƙasar Mali an kammala shirin zabe

August 9, 2013

'Yan takaran zaben zagaye na biyu a Mali wato Keita da Cisse kowa ya bayyana manufofinsa.

A man casts his ballot during Mali's presidential election in Lafiabougou in Bamako, July 28, 2013. Voters in Mali headed to the polls on Sunday in a presidential election it is hoped will provide a fresh start to a country divided by a coup and a war in its desert north. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: ELECTION POLITICS)
Präsidentschaftswahl in MaliHoto: Reuters

A ranar Lahadi 11 ga wannan wata na Augusta 'yan Mali za su sake zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kasarsu a zagaye na biyu, tsakanin Ibrahim Boubakar Keita da Soumaila Cisse, ana dai kallon wannan zabe a matsayin zakaran gwajin dafi tsakanin 'yan takarar guda biyu.

Jadawalin zaben Soumaila Cisse ya kunshi bangarori guda biyar kamar haka, kafa hukumomi masu karfin gaske, habaka tattalin arzikin kasa, sannan da wasu aikace- aikace da ya ce zai gudanarwa na kyautata rayuwar al'umma. A kan maganar zaman kashe wando da mafi yawa daga cikin matasan Mali ke fama da shi, dan takara Soumaila Cisse yi alkawarin samarwa matasa ayyukan yi kusan dubu dari biyar a cikin shekaru biyar masu zuwa. Mamadou Thiam dan majalisar dokoki ne a bangaren jam'iyar URD ta Soumaila Cisse.

Ibrahim Boubacar Keita, Dan takara na gaba a zaben MaliHoto: Katrin Gänsler

"Ya ce, a cikin jadawalin zabensa ya yi alkawarin samarwa matasa ayukan yi kusan dubu dari biyar a cikin shekaru biyar masu zuwa, ya ce dama ai ya saba fadin cewa, rashin aikin yi ga matasa tamkar wani bom ne a danne, idan ya kasance matasan na gararamba a kan titina, saboda akwai hadarin su saki hanya."

A bangaren dan takara Ibrahim Bubakar Keita kuma, a nan an yi alkawarin cewa, za a yi yakin tukuru da matsalar cin hanci da rashawa da kirkiro hanyoyin da za su habaka tattalin arzikin arewacin kasar ta Mali, sannan an yi alkawarin kirkiro ayyukan yi kusan dubu dari biyu a shekaru biyar masu zuwa, hakan kuma shi ne abinda mai hankali zai iya amincewa da shi, idan aka dubi irin kalubalen dake gaban wannan kasa, a cewar Ahmadou Sangare kakakin Ibrahim Boubakar Keita.

Soumaïla Cissé, Wanda ya zo na biyu a zaben MaliHoto: Katrin Gänsler

"Ya ce, a kan maganar zaman kashe wando akwai wani tsari da zai tantance matasa domin samar masu ayyukan yi, muna bukatar bunkasa ayyuka a dukkanin yankunan kasar Mali, an yi maganar ayyuka dubu dari biyu, domin ba za mu sa adadin da ya wuce kima ba, ya ce IBK ya fada mana cewa, mu tafi a kan tsari na gaskiya tare da tunanin cewa, kasar Mali na da bukatoci masu yawan gaske. Akwai matsalolin da suka shafi kiwon lafiya, akwai kuma matsalolin da suka shafi ilimi, sannan sojojinmu na bukatar kayakin aiki kenan akwai bangarori da dama masu mahimmanci."

A kan maganar shawo kan matsalar Abzinawa, ko wane alkawari bangaren dan takara Cisse ya yi, ga amsar da Mamadou Thiam ya bayar.

"Ya ce tare da la'akari da dunkulewar kasa, ta haka ne za a iya tattaunawa a kan tsarin baiwa ko wane yankin yancin cin gashin kansa da kuma za a fadada wannan tsarin, sannan ko wane yanki ya ci moriyar arzikin kasa, tare da aiki da kwarewa."

Magoya bayan yan siyasa a MaliHoto: DW/K.Gänsler

To ko a bangaren dan takara Ibrahim Boubakar Keita ta wacce hanya zai tunkari wannan matsala ta Abzinawa, ga amsar da Ahmadou Sangare ya bayar.

"Ya ce matsalar Abzinawa za a shawo kanta ne ta hanyar tattaunawa da kungiyoyin mazauna arewacin kasa, tattaunawar da kuma za ta baiwa 'yan kasar Mali damar bayyana ra'ayoyi tsakaninsu ba tare wani damun kai ba, domin gano hanyoyin magance matsalar arewa."

A gaskiya tsakanin jidawalin zaben dan takarar mai ra'ayin gurguzu Ibrahim Boubakar Keita, da dan takarar mai ra'ayin jari hujja Soumaila Cisse babu wani bambaci na a zo a gani, saboda ko wanne daga cikinsu ya mayar da hankali ne a kan bukatocin 'yan kasar Mali, alalmisali Ibrahim Boubakar Keita na maganar karfafa matakan tsaro, shi kuma Soumaila Cisse ya na maganar sabunta bangaren na tsaro, sannan inda Soumaila Cisse ke maganar kara kyautata jin dadin jama'a, shi kuma IBK ya yi alkawarin kara kaso a bangaren.

Mawallafi: Youssoufou Abdoulaye
Edita: Usman Shehu Usman