1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A China an daure tsohon babban jami'in gwamnati

Suleiman BabayoJune 11, 2015

An daure tsohon babban jami'in tsaron China rai-da-rai saboda cin hanci

China Zhou Yongkang in Peking
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Ng Han Guan

A kasar China na daure tsohon babban jami'in hukumar tsaron kasar Zhou Yongkang, na tsawon rai-da-rai saboda an same shi da karbar cin hanci da rasha da kuma amfani da mukamunsa ta hanyar da ta saba doka, inda ya kwarmata bayanan asiri. Kafofin yada labaran kasar sun ce za a kwace dukiyar Mr Zhou dan shekaru 72 da haihuwa. Tun cikin watan Afrilu aka fara shari'ar kuma tsohon jami'in ya amince da laifuka 22 da aka tuhume shi, idan ya ce bai zai daukaka kara ba.

Wannan shari'a ana gani ta zama nasara ga Shugaba Xi Jinping na kasar ta China wanda ya dauki matakin yaki da cin hanci da rashawa tsakanin manyan jami'an gwamnatin kasar.