A cimma matsayar kafa gwamnati a Kwango
July 26, 2019Gamayyar jam'iyun siyasa da ke goyon bayan shugaban Kwango Felix Tshisekedi da kuma takwarta da ke goyon baya wanda ya sauka daga mulki Joseph Kabila sun sanar da cimma yarjejeniyar kafa gwamnati hadin gwiwa bayan kwashe watanni shida na tattaunawa tsakaninsu. Bangarorin biyu sun bayyana cewar sabuwar gwamnatin za ta kunshi ministoci 65, inda 23 za su fito daga bangaren shugaba Tshisekedi yayni da 42 za su zama na bangaren Kabila, lamarin da ke nuna cewa tsohon shugaba kasa ya fi samun kaso mai tsoka.
Sai dai bangarorin Tshisekedi da na Kabila ba su yanke shawara a kan wadanda za su rike manyan ma'aikatu ba kama daga na cikin gida har i zuwa ga na kudi da na ma'adinai. Amma cikin wata hira da yayi da kafofin watsa labarai na Faransa, Shugaban Kwango Felix Tshisekedi ya ce zai sa ido wajen zaban wadanda za su rike ma'aikatun da aka fi ji da su. Tun dai ranar 24 ga watan Janairu ne aka rantar da Felix Tshisekedi ba tare da ya yi nasarar kafa gwamnati ba.