A haramtawa Moroko shiga gasar kofin Afirka
November 11, 2014Talla
Wata sanarwa da hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta fitar bayan kammala taro a birnin Alkhira na kasar Masar, ta bayyana cewa tunda dai Moroko ta fasa karban bakwancin gasar cin kofin kwallon kafan Afirka to kuwa ba za ta shiga gasar ba. Moroko dai ta sanar da cewa, ta fasa karban bakwancin gasar, a wani abin da gwamnatin kasar ta ce, wai tsaron bazuwar cutar Ebola ne yasa. Yanzu haka kungiyar CAF na ci gaba da tantance wata kasa da za ta karbi bakwancin gasar a bana.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo