1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman ci gaba wayar da kan al'umma kan illolin cutar

Salissou Boukari
May 5, 2020

Kwanaki kalilan da rasuwar ministan kwadago na Jamhuriyar Nijar Mohamed Ben Omar, 'yan kasar na ci gaba da nuna mabanbantan ra'ayoyi kan lamuran da suka shafi cutar COVID-19.

Niger Niamey Frau mit Schutzmaske
Hoto: Imago Images/Le Pictorium

A Jamhuriyar Nijar kwana daya bayan jana'izar ministan ma'aikatan kwadago na kasar Mohamed Ben Omar, wanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon cutar nan ta Coronavirus, har yanzu ra'ayoyi na bambanta kan yadda ‘yan kasar ke kallon wannan cuta, inda wadanda suka yarda da sahihancin cutar ma ke da shakku a wasu fannoni, lamarin da ke nunin cewa har yanzu da sauran rina a kaba wajen wayar da kan mutane dangane da cutar ta Covid 19.

Duk da cewa a kullu yaumin dubban  mutane ne ke mutuwa a fadin duniya sakamakon wannan Cutar, musamman ma a manyan kasashe irin na Turai da Amurka, amma a kasashen Afirka, musamman ma Nijar mutane na ci gaba da nuna turjiya dangane da matakan da suka kamata kowa ya dauka na kariya.

Hoto: DW/M. Kanta

Tun dai da jimawa ne ma'aikatu da dama na gwamnati zuwa masu zaman kansu suka dauki matakai na kaucewa yaduwar wannan cuta a tsakanin al'umma, kuma rasuwar Minista Ben Omar wanda ba da dadewa ba shi kanshi ya yi jan hankali ga ma'aikata kan cutar, ana ganin za ta sanya wasu ‘yan kasar su shiga taitayinsu. 

Ko shi kanshi ciwon majina ko mura da aka sani, ciwo ne da ke galabaitar da jama'a kuma ya kan yadu ne a tsakanin al'umma sanadiyar rainashi da ake yi da cewa karamin ciwo ne, ba tare da daukar matakan kariya ba.

Iri-irin wannan lamari dai da kan sa wa mutane nuna turjiya ko son kai wajen amincewa da kasancewar shi kanshi ciwon na Coronavirus, a cewar masu lura da al'amuran yau da kullum, ya samo asali ne kan yadda ake saku-saku wajan hukunta masu aikata laifi musamman ma idan sun shafi bangaran gwamnati, inda ‘yan kasar da dama ke ganin cewa ba daya suke a gaban doka ba ma'ana akwai shafaffu da mai lamarin da ke kara sanya tazara tsakanin wani bangare na al'umma da masu fada a ji na bangaran gwamnati ko da kuwa abun da suka fada gaskiya ne.