1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A kalla mutum 23 sun mutu bayan tashin bam a Maiduguri

March 17, 2026

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Bono ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin da dare.

Yadda ma'aikata ke kwashe mutane da suka mutu a harin bam a Maiduguri
Yadda ma'aikata ke kwashe mutane da suka mutu a harin bam a MaiduguriHoto: AFP

Akalla mutum 23 ne suka mutu, yayin da 108 suka jikkata a wasu hare-haren kunar bakin wake guda uku da aka kai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar 'yan sanda a jihar ce ta tabbatar da mutuwar mutanen a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Harin bam ya halaka mutane a jihar Bornon Najeriya

Lamarin ya faru ne jim bayan buda baki a wurare daban-daban na birnin ciki har da kasuwar Monday market da ofishin kiran waya da aika sakonni na Post Office da kuma Asibitin Koyarwa na Maiduguri.

Jihar Borno ta shaida karuwar matsalar tsaro a baya-bayannan musamman daga wadanda ake zargi 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.

Matasa na dari-dari da shiga aikin soja a Najeriya

Ko da a farkon watan nan mayakan sun sanar da kwace garin Ngoshe a jihar ta Borno tare barazanar yin Idin karamar sallah a can.