A Kamaru CPDM ta cika shakaru 30
March 24, 2015 An dai somo shagulgulan wannan biki ne daga birnin Maroua da ke arewacin ƙasar ta Kamaru, inda jiga-jigan jam'yiyyar suka yi ta bayyana irin nasarar da jam'iyyar ta samu ta samu a waɗannan shekaru. Sai dai jam'iyyun adawa a ƙasar sun ce al'umma ba su gani a asa ba a wadannan shekarun 30 da CPDM din ta yi tana mulki, kana shugabanta Paul Biya, bai aikata komai ba sai ma dai ci-gaba da kan-kane madafun iko da ya ke yi.
Ita dai jam'iyyar CPDM ko kuma RDPC na ganin cewa ita ce ta kawo mulkin dimokaraɗiyya a Kamarun kamar, yadda mataimakin magajin garin Yaounde Falalu Mijin Yawa ya bayyana wa tashar DW, inda ya ce da jam'iyar ita daya tilo ake da ita ƙasar, amma yanzu ta haifi jam'iyyu sama da 50, don haka jam'iyyar na mai alfaharin kawo dimokradiyya a Kamaru. Amma cewar Alhaji Sani matan Hausa da ke jam'iyar adawa ta UMS, ya ce babu yadda za'a yi ace CPDM ta kawo dimokradiyya a Kamaru. Hasali ma jam'iyyar ita ce ta rusa tsarin demokradiyya, ganin yadda ta kan/kane mulkin kasar tun bayan samun yancin kai a shekara ta 1960. Idan ma ana batun jam'iyyar CPDM a cewar Alhaji Sani, sai a ce demokradiyya ba ta ma fara ba a ƙasar. Sai dai kawai za'a yi batu cewa Kamaru na da jam'iyyu barkatai, amma kuma ko suna da tasiri a tafiyar da mulkin kasar, wannan shi ne abun tambaya.
A cewar 'yan adawa, shekaru 30 da jam'iyyar CPDM ta yi tana mulki ƙarƙashin gwamnatin Paul Biya, ba abinda ta kawo illa koma bayan tattalin arziki, inda Kamaru a yanzu ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta a duniya. Alhali kuwa suka ce lokacin marigayi tsohon shugaban ƙasar Alhaji Ahmadou Ahidjo, ya miƙa wa Paul Biya mulki, ƙasar na da watar tattalin arziki. Inda Ahidjo ya bar manyan kamfanonin sama 50 a kasar da kamfanonin jiragen sama da na ruwa, abin da kuma yanzu 'yan adawa ke ganin duk sun zama tarihi a Kamaru.
Amma cewar wadanda ke kan mulkin ƙasar, Kamaru ta samu gaggarumin ci-gaba ta fannin ilimi da kiwon lafiya, domin a yanzu akwai ƙananan asibitoci a karkara, ga kuma batun ruwan sha ƙasar Kamaru sambarka. Haka zalika lokacin da marigayi Ahidjo ya mika mulki wa shugaba Paul Biya, kasar na da jami'a daya kacal, amma yanzu suna da jami'o'i dayawa, ga kuma an bai wa 'yan kasuwa masu zaman kansu ɗamar kafa jami'o'i.
Ƙasar Kamaru da ke da yawan mutane miliyan 21, na daga cikin ƙasashen Afirka da shugabanninsu suka shafe shekara da shekaru suna kan gadon mulki.